Matakan yaki da ta'addanci daga hukumomi a Bauchi
April 10, 2014 Wasu al'ummomn yankin kananan hukumomin Darazo da Ganjuwa dake jihar
Bauchi a Arewa maso gabas a tarayyar Najeriya ana zaman zullumi a sakamakon
ganin shige da fice na wasu mutane da ba a tantance ko su wanene ba, dake
zaune a cikin dazuzzukan a wadannan yankunan, jama'a dai sun koka dan gane
da fashi da makami tare da sace-sace da yin garkuwa da wasu fitattun yan siyasa
a 'yan makwannin da suka gabata, kamar yadda wani dan yankin ya shaida min.
Hakazalika Alhaji Abdulrahaman Isa Baba hakimain Soro yace an umarce su da
su rika yin rahotoakan duk wani bakin haure da ya iso yankin.
Jami'an tsaro a jihar ta Bauchi sunce suna da labarin zargin cewa ana ganin wasu
mutane da makamai a wannan yanki amma suna iya kokarinsu da goyon bayan al'umma suga cewa sun yi maganin lamarin kamar yadda kwamishinan yan sanda Muhammed Ladan yayi bayani.
Ko da yake shugaban kasa Goodluck Jonathan ya jaddada aniyar gwamnatinsa ta kauda barazanar ta'addanci a jihohin arewa, a wata ziyara da ya kawo Bauchi
kusan makwanni biyu da suka gabata, amma har yanzu bata canza zane ba domin kuwa bayan kalaman nasa, a kalla anyi asarar rayuka fiye da dari biyu a jihohin Zamfara, Yobe Borno, Nasarawa da Taraba a cikin makwanni biyu kacal, ko a farkon wannan mako sai da aka bindige wasu yan sanda bakwai a garin Gwaram a jihar Jigawa.
Mawallafi: Ado Abdullahi Hazzad
Edita: Umaru Aliyu