1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matakin ƙungiyar haɗa kan Larabawa kan Siriya

November 17, 2011

Bisa ga dukkan alamu ƙungiyar haɗa kan ƙasashen Larabawa ba ta da abin da zata yi dangane da Siriya illa ta ci gaba da barazanar ƙaƙaba wa ƙasar takunkumi kawai

Shugaba Bashar al-Assad na SiriyaHoto: picture-alliance/dpa

Ƙungiyar haɗin kan Larabawa ta farga da alƙiblar da aka fuskanta, inda ta fito fili tana mai nuna wa shugaba Bashar al-Assad kan bindiga, ko dai gwamnatinsa ta cika sharuɗɗan shirin zaman lafiyar da aka zayyana ko kuma a ƙaƙaba wa gwamnatinsa takunkumi. Buƙatar da ƙungiyar ta gabatar dai shi ne game da sakin illahirin fursinonin siyasar dake tsare nan da ƙarshen mako da janye sojojin Siriyar daga biranen ƙasar. Domin bin diddigin cika wannan sharaɗi za a tura wata tawagar masu sa ido zuwa ƙasar ta Siriya. Amincewa da wannan buƙatar ne kawai za ta ba wa Siriyar kafar sake komawa inuwar ƙungiyar ta haɗin kan Larabawa.

Ƙasashen na Larabawa dai sun dage ne akan bakansu tare da tsawata wa shugaba Assad. Tun ma dai a farkon wannan makon ne ƙungiyar tarayyar Turai ta ƙakaba wa Siriya wasu sabbin matakai na takunkumi, abin dake ƙara jefa shugaba Assad cikin mawuyacin hali na ƙaƙa-nika-yi. To sai dai kuma shugaban na Siriya sai ƙara tsawwala matakan muzantawa yake yi domin mayar da martani akan matsin lambar da yake fuskanta. A ranar litinin kaɗai kimanin mutane saba'in aka kashe sakamakon tashe-tashen hankula. Wannan adadin kuwa shi ne mafi tsanani tun bayan ɓillar zanga-zangar adawar a Siriya misalin watanni takwas da suka wuce.

Ci gaba da tashintashina a Dara'a ta ƙasar SiriyaHoto: dapd

A kuma wannan makon an samu rahotannin kai farmaki kan ofisoshin jakadancin wasu ƙasashe na ƙetare, ba ma na ƙasashen yammaci kaɗai ba, abin ya haɗa har da ofishin jakadancin ƙasar Jordan. Hakan na ɗaga cikin abin da ya sanya sarki Abdallah na biyu ya fito ƙarara yana mai kiran shugaba Assad da yayi murabus. To sai dai kuma duk da matsin lambar da Siriya ke fuskanta daga ƙetare da kuma korarta daga ƙungiyar haɗin kan Larabawa da aka yi, har yau maganar katsalandan soja a ƙasar ba ta taso ba. Hatta ita kanta ƙungiyar haɗin kan Larabawan sai da ta bayyana hakan a taronta na birnin Rabbat. Akwai dalilai masu tarin yawa da suka sanya ba za a iya ɗaukar matakan soja akan Siriya kamar yadda lamarin ya kasance dangane da Libiya ba. Babu ɗaya daga cikin ƙasashen dake maƙobtaka da Siriyar, kama daga Isra'ila zuwa Turkiyya da sauran ƙasashen Larabawa dake sha'awar katsalanda A ƙasar, musamman domin gudun tsudumar ƙasar cikin wani yaƙi na basasa. Ta la'akari da haka ba a da tayi illa a cikin gaba da matsin lamba, ko da yake ba tabbas ko kwalliya zata mayar da kuɗin sabulu bisa manufa.

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Yahouza Sadissou Madobi