Matakin da Turkiya ta ɗauka a kan Isra'ila
September 2, 2011Ƙasar Turkiya ta kori jakadan Isra'ila a Istanbul tare da katse jerin yarjeniyoyin da ke tsakaninta da bani yahudu a fannin tsaro, sakamakon jan kunnen da Majalisar Dinkin duniya ta yi wa ɓangarorin biyu a rikicin jigilar kayan agaji zuwa zirrin Gaza da aka fiskanta. Rahoton da Majalisar Ɗinkin duniya ta fitar ya nunar da cewar sojojin kundunbalan Isra'ila sun wuce gona da iri, lokacin da suka yi dirar miƙliya a kan jirgin ruwan Turkiya da ke kai kayan aagajin zirin gaza a watan mayun da ya gabata. Sai dai kuma ta bayyana cewar killace zirin gazan da isra'ila ke yi bai saba ma dakokin kasa da ƙasa ba.
Mutane tara ne dai suka rasa rayukansu ciki kuwa har da 'yan Turkiya takwas. Ita dai fadar mulkin Istanbaul ta nemi Isra'ila ta roƙi gafara game da kai hari da ta yi a kan jirgin ruwan. Sai dai ofishin firaminista Benjamin Netanyahu ya bayyana cewar ya na ci gaba da gudanar da shawarwari domin bayyana matsayin gwamnatin Isra'ila game da wannan batu.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Usman Shehu Usman