Matakin Eu a kan Kungiyar Hezbollah
July 22, 2013Ministocin harkokin wajen Eu ne suka yanke wannan hukunci a taron da suke gudanarwa a birnin Bruxelles, shakara guda bayan harin da 'yan bindigan Hesbollah suka kai a filin saman Burgas na Bulgariya a ranar 18 ga watan Yulin 2012.
Mutane da dama ne suka kwanta da dama a wannan hari ciki kuwa har da dan Bulgeriya daya, da kuma 'yan Isra'ila biyar. Ko da shi ma ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle, sai da ya ce bai kamata a kyalle reshen kungiyar Hezbollah da ke dauke da makamai ya aiwatar da hari a wata kasa ta nahiyar Turai ba tare da daukan mataki a kanta shi ba.
Kungiyar ta Gamayyar Turai ta kuma haramta wa jami'an masana'antu da kuma kungiyoyi da ke da alaka da Hezbollah shigowa nahiyar Turai tare kuma da toshe kafofinsu na ajiyan kudi a bankunan Turai.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Saleh Umar Saleh