Tattalin arziki
Ganda na samun karbuwa a Najeriya
Muhammed Bello Ibrahim AMA/LMJ/SB
June 29, 2023Talla
Cimakar Ganda na samun karbuwa ga dumbin al'umma a sassan Afirka. Wannan ta sanya, cibiyar gashin Gandar, dake a mayankar dabbobi ta Fagge a jihar Kano ke ci ba dare ba rana. Suna yin hadin gandar da fatar dabbobi kamar Rakumi, Saniya, Awakai da sauransu. Sannan matasa ne suka fi cin gajiyar sana'ar, domin su akwai ɗari ruwansu, dake cin abinci.