1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Sweden ta shiga NATO

Suleiman Babayo ZUD
March 5, 2024

An shiga matakin karshen na shigar da Sweden cikin kungiyar tsaron NATO/OTAN bayan shugaban kasar Hangari ya saka hannu kan dokar shigar da Sweden cikin kungiyar tsaron mai muhimmanci game da tsaro ta duniya.

Shugaba Tamás Sulyok na kasar Hangari
Shugaba Tamás Sulyok na kasar HangariHoto: Szilard Vörös/estost/IMAGO

A wannan Talata Shugaba Tamás Sulyok na kasar Hangari ya saka hannu kan dokar shigar da Sweden cikin kungiyar tsaron NATO/OTAN. Haka na zuwa bayan majalisar dokokin kasar ta Hangari ta kada kuri'ar shigar ta kasar ta Sweden cikin kungiyar ta NATO ranar 26 ga watan jiya na Febrairu, abin da ke zama babi na karshe na shigar da Sweden cikin kungiyar bayan daukacin kasashe mambobi sun yi haka tun da farko.

Babban sakataren kungiyar ta NATO, Jens Stolltenberg zai gayyaci kasar Sweden a hukumance ta shiga kungiyar tsaron mai matukar tasiri a duniya.

Tuni  Pal Jonson ministan tsaron kasar ta Sweden ya yi maraba da wannan mataki. Haka ya kawo karshen shekaru biyu na matakin shigar da kasashen Finland da Sweden cikin kungiyar tsaron NATO tun bayan kutsen da Rasha ta kaddamar kan kasar Ukraine.