Talla
Mahukuntan kasar Isra'ila sun tsaya kan matakin korar Afirkawan da ke zama a kasar. Faraministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, wanda ya shaidar da hakan ya bayyana bakin hauren a matsayin 'yan kutse' ga Isra'ilar’ Firaministan ya shaida haka ne lokacin wani zaman da majalisar zartaswar kasar ta yi.
A nasu bangaren, bakin hauren, suna zargin Isra'ila tana son tura su zuwa kasashen Yuganda da Ruwanda.
Kasar dai ta yi tayin bai wa 'yan hijran dala $3,500 da kuma daukar nauyin tikitin komar da su kasashen da suka fito.