1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Matakin neman rusa majalisar dokokin Senegal

September 5, 2024

Shugaba Bassirou Diomaye Faye na kasar Senegal ya shirya rusa majalisar dokokin kasar wacce ‘yan hamayya ke da rinjaye a cikinta.

Senegals neu gewählter Präsident Bassirou Diomaye Faye
Hoto: Zohra Bensemra/REUTERS

Matakin da ake ganin zai iya kasancewa cikin ‘yan kwanakin da ke tafe, ya zo ne daidai lokacin da gwamnati mai ci a Senegal din ta kaddamar da wani kamfe na yaki da rashawa da ke sa ido kan wasu gommai a kasar. Watsi da kudirin gyaran fuska ga kundin tsarin mulki da majalisar dokokin Senegal ta yi ne ummal aba'isan rikicin da ya kunno kai tsakaninta da bangaren zartasawa. Shugaban kasar Senegal Bassirou Diomaye Faye ya ba da shawarar soke wasu hukumomi na gwamnati sakamakon yawan kudi da ake kashewa wajen aiwatar da su, wadanda suka hada da majalisar tattalin arziki da fannin zamantakewa da muhalli da kuma hukumar da ke kula da kananan hukumomi.

Karin Bayani: Shirin rusa majalisar dokokin Senegal

Hoto: John Wessels/AFP/Getty Images

Har yanzu, 'yan adawa ne ke da rinjaye a majalisar dokokin Senegal, lamarin da ke kawo cikas ga yunkurin gwamnati na kwaskware wasu dokoki da za su ba ta damar aiwatar da manufofinta. Saboda haka ne majalisar ta kudiri aniyar tsige firayiminista Ousmane Sonko saboda kin hallara a gabanta domin bayyana manufofin gwamnatinsa. Shugaba Bassirou Diomaye Faye dai ya tuntubi kotun tsarin mulkin Senegal domin sanin lokacin rusa majalisar dokoki domin a gudanar da zaben gaba da wa‘adi ya yi, da fatan samun rinjaye ‘yan majalisar dokoki da zai dogara a kansu wajen kawo sauyin da ya yi alkawari.

A karkashin kundin tsarin mulkin Senegal dai, shugaban kasa na iya rushe majalisar dokoki ne kawai bayan shekaru biyu da kafa ta. Wannan na nufin cewar Shugaba Diomaye Faye zai iya daukar wannan mataki daga ranar 12 ga watan Satumba, bayan ya samu matsayi ko shawarar kotun tsarin mulki da ya riga ya tuntuba. Yanzu haka wani dan majalisar adawa na kasar ta Senegal  ya sanar da shigar da kara, kan wani kudiri na tsike gwammnatin firaminista Ousmane Sonkon da aka yi.

Ana dai kallon wannan sabon rikicin siyasa a matsayin wani abin da ke iya fashewa nan da kowane lokaci, saboda gwamnatin firaministan ba ta da rinjaye a masjalisar. A fili yake dai, barazanar bangaren adawa a Senegal ya ja harkokin gwamnati baya, ganin cewa har ya zuwa wannan lokacin, babu wani bayani kan abin da ya shafi gwamnati da firamninistan Ousmane Sonko ya iya gabatar wa majalisar dokoki.