Matakin Tarayyar Turai bayan arangama a Kiev
February 19, 2014Adadin wadanda suka rasa rayukansu a arangamar da ta gudanar tsakanin 'yan adawan Ukraine da kuma 'yan sandan kasar bai tasamma 26 ba. Amma kuma har yanzu akwai shinge da ke raba sassa biyu a dandalin 'yanci na birnin Kiev. Kana dubban mazauna babban birnin na Ukriane suna ci-gaba da kai ma wadanda suka jikata wadanda adadinsu ya kai 241 dauki. Wannan rikici na siyasa dai shi ne mafi muni da Ukraine ta fuskanta tun bayan samun 'yancin kanta shekaru 23 ke nan da suka gabata. Tuni dai sakataren zartaswa na Kungiyar Gamayyar Turai Jose Manuel Barosso ya bukaci bangarorin biyu da ke gaba da juna da hawa kan teburin tattaunawa.
"Muna kira ga bangarorin biyu da ke gaba da juna da kawo karshen tashin hankali ba tare da bata lokaci ba, tare da hawa kan teburin tattaunawa domin gano bakin zaren warware rikicin. Ta wannan hanye ce kawai za a mutunta 'yancin 'yan Ukraine tare da samar da sahihiyar demokaradiya."
Ummal aba'isan tashin hankali a Ukraine
Tun dai daga daren talata zuwa larabe ne aka fara bata kashi tsakanin jami'an tsaro da kuma wadanda ke neman shugaba Viktor Ianoukovitch ya sauka daga kujerar mulki. Suna zarginsa da yin burus da bukatarsu ta shigar da kasar ta Ukraine cikin Kungiyar Gamayyar Turai. Sai dai sabanin haka, shugaban Ianoukovitch ya kulla kawance ne da kasar Rasha: lamarin da ya harzika wadanda ke adawa da manufofinsa, a inda suka shafe makwani suna kalubalantar gwamnatinsa a dandalin 'yanci na birnin Kiev. Inda gizo ke saka shi ne so da dama shugaban na Ukraine ya bai wa 'yan sanda izinin amfani da karfi wajen tarwatsa masu zanga-zanga. Saboda haka ne Jose Manuel Barasso na EU ya ce Turai ba za ta kyalle wannan al'amari ba tare da daukan matakin ladabtarawa ba.
"Mun fada da babbar murya cewa Kungiyar Gamayyar Turai za ta dauki matakan da suka wajaba idan rikicin ya dauki wani salo. saboda haka ne muke jira kasashe membobin Eu su dauki matakan ladabtar da wadanda suka ba da umurnin far wa masu zanga-zanga."
Takakumin Eu a kan jami'an gwamnati
Jakadun kasashen Turai a Eu sun gudanar da wani taron gaggawa a birnin Bruxelles domin tattaunawa game da matakan da ya kamata a dauka a kan shugaba Viktor Ianoukovitch da mukarrabansa. Kawo yanzu dai ba a san irin takunkumin da EU za ta aza wa shugaban na Ukraine ba. Amma dai a tabbatar da cewa zai fara aiki ne a ranar jumma'a idan Allah ya yarda. Ma'ana bayan taron musamman da ministan harkokin wajen Turai za su gudanar a gobe alhamis domin duba halin da ake ciki a Kiev da kuma nazarin matakan da ya kamata a dauka.
Kasashen Jamus da Faransa da kuma Poland ne suka nemi a aza wa shugabannin na ukraine takunkumi na hana shigowa Turai tare da soke duk ajiyan da suke da shi a kasashen da ke da kujera a EU. Suna zargin Ianoukovitch da mukarrabansa da alhakin rikicin. Ko da shi ma Ruslana Lyschytschko mawaki kana dan adawa a Ukraine, sai da ya dora alhakin abin da ke faruwa kan Ianoukovitch.
"Jami'an gwamnati ne ummal ab'isan tashin hankali da ya gudana a Kiev. Shugaba Viktor Ianoukovitch ne ya ruruta wutar wannan tashin hankali. Shi ne ya zuba yan bangan a kan titunan Kiev. Sannan kuma jami'an tsaro da dama sun yi shigar shigar burtu a inda suka hautsunu da masu zanga-zanga a dandalin Maidan."
Kasar Rasha ta yi tir da abin da ta kira yunkurin juyin mulki da 'yan adawa suka yi a Ukraine, tare da kiransu da kawo karshen wadannan tashe-tashen hankula.
Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Zainab Mohammed Abubakar