Matan da aka sace a jihar Borno sun zarta 100, in ji hukuma
March 7, 2024![Mata na shiga tasku sakamakon matsalar tsaro a arewacin Najeriya](https://static.dw.com/image/39962583_800.webp)
Jami'in yada labarai na karamar hukumar Ngala Ali Bukar ya bayyana wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa mazauna kauyen sun tabbatar da bacewar mutane 113 a halin yanzu. Dama ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya (OCHA) ya ce an yi garkuwa da mata sama da 200 da ke zaune a sansanonin ‘yan gudun hijira a lokacin da suka je neman itace.
Karin bayani: Kokarin magance tsaro a arewacin Najeriya
Satar mutane don neman kudin fansa na ci gaba da zama babbar matsala a yankunan Arewa maso Yamma da Arewa maso gabashin Najeriya. Shugabannin mayakan sa-kai na zargin kungiyar ISWAP da marar hannu a satar mutane. Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya hau karagar mulki ne a 2023 ya yi alkawarin magance tabarbarewar tsaro da kuma barkewar rikicin kabilanci a jihohin tsakiyar kasar.
Karin bayani: Najeriya: Ina kudaden fansa suke shiga?
A Jihar Borno dai, ayyukan ta'addanci sun yi sanadin mutuwar mutane sama da 40,000 tare da raba miliyan biyu da muhallansu a cikin shekaru 15 da suka gabata.