1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matan Masar sun shiga zanga-zanga

December 21, 2011

A matsayin martaninsu ga wulakancin da wata mata ta fuskanta a hannun dakarun tsaro mata sun shiga zanga-zang a kasar Masar

An Egyptian protester throws a stone toward soldiers, unseen, as a building burns during clashes near Tahrir Square, in Cairo, Egypt, Saturday, Dec. 17, 2011. Hundreds of Egyptian soldiers swept into Cairo's Tahrir Square on Saturday, chasing protesters and beating them to the ground with sticks and tossing journalists' TV cameras off of balconies in the second day of a violent crackdown on anti-military protesters that has left nine dead and hundreds injured. (Foto:Ahmad Hammad/AP/dapd)
Arangamar dakaru da 'yan zanga-zangaHoto: dapd

Dubban mata a kasar Masar sun fantsama a dandalin Tahrir da ke a birnin Alƙahira domin nuna ɓacin ransu dangane da cin zarafin da jami'an tsaron suka yi wa wata mata a lokacin zanga-zanga. Matar wacce 'yan sanda suka riƙa ja a ƙas wadda kuma suka yi wa kusan tsirara an yi ta baza bidiyonta da hotunanta a gidajan telbijan na duniya. Sakatariyar harkokin wajen Amirka Hilary Clinton ta bayyana takaicinta tare da yin Allah wadai da abin da ya faru. Sannan kuma ta yi kira ga hukumomin soja da su mutunta 'yanci walwala na jama'a.

Matan sun gudanar da zanga-zanga ne duk kuwa da cewar majalisar ƙoli ta mulkin sojin ta nemi ahuwa akan abinda ta kira kuskure. Kawo yanzu dai mutane guda 14 suka rasa rayukansu a cikin boren da jama'ar suke yi na neman ganin sojojin sun gaggauta miƙa mulki ga farar hula.

Mawallafi:Abdourrahamane Hassane
Edita: Halima Balaraba Abbas