1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Mata na zanga-zangar neman hakki

Uwais Abubakar Idris MAB
March 2, 2022

Daruruwan mata masu rajin kare hakkokinsu sun nuna wa majalisar dokokin Najeriya bacin ransu a kan watsi da ta yi da kudurorin da ke bai wa mata karin madafan iko a siyasa, inda suka nemi da a sake gyara wadannan sassa.

Nigeria Taraba Staat Frauen
Matan Najeriya na fitowa kada kuri'a, amma ba su cika samun manyan mukamai baHoto: Picture alliance/dpa/epa/G. Esiri

Kungiyoyin mata sun rinka rera takensu a fusace don nuna rashin yarda da abin da suka kira nuna son kai da ‘yan majalisa suka yi musu a lokacin gyaran fuska a tsarin mulkin Najeriya. Kudurori biyu ne dai 'yan majalisar suka yi watsi da su da suka shafi mata: Na farko shi ne wanda ya so ya sanya mata zama mataimaka a shugabancin jam'iyyu, da kuma kudurin da ya nemi ba su karin wakilci a takarar zama ‘yan majalisa.

Shin me ya yi zafi har ya kai ga fitowar mata?

Mataimakin shugaban Najeriya Osinbajo ya karbi bakunci Amina Mohammed ta MDDHoto: Novo Isioro

Dr Jophia Gupar wacce ke daya daga shugabanin matan da ke zanga-zanga ta ce "Ba mu ga dalilin da zai sa majalisar dokoki ta Najeriya ta ki amincewa da abubuwan da mata ke so ba... Muna so suka sake duba abubuwan da mata suka ce a yi musu."

Matan sun shirya zaman dirshen a kofar shiga majalisar, lamarin da ya kawo cikas ga ayyukanta. Sai da a tilas aka rufe kofar majalisar a kan wannan batu na mata da ke daukar hankali a Najeriya. Niri Goyit da ke wakiltar kungiyar mata ta Women for Women da kuma Action Aid ta ce: "Aikin da ake yi ba mata, ba aiki mai kyau ba ne. Mu kuma ba mu da wata kasa baya ga Najeriya."

Majalisa ta kwantar wa matan da hankali

Majalisar dokokin Najeriya na jan aiki a kan batutuwan da suka shafi mataHoto: cc-by-sa/Shiraz Chakera

Mataimakin shugaban masu rinjaye a majalisar Sanata Robert Ajayi Boroffice ya jagoranci ‘yan majalisa don yi wa masu zanga zangar jawabi yana cewa: " Mun zo nan don mu saurare ku ta yadda za'a samu maslaha, ku sani matakin da aka dauka ba yana nufin wannan sashe da aka so yi wa gyara ba ya da muhimmanci ba ne."

Sai dai bayan wannan jawabi matan suka ce ba su fa yarda ba. Akwai dai matan da suka yiwo takakka daga yankunan Abujan a kan wannan batu irin su Safiyyah Tijjani. A bayyane take cewa matakin da ‘yan majalisar suka dauka ya yi wa matan Najeriyar zafi.