1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matar da lashe lambar yabo ta Nobel ta shawarci kasashe

December 10, 2025

Matar da lashe kambun Nobel na bana, ta ce lallai ne kasashen duniya masu bin tsarin mulki, su mike tsaye don kare 'yanci da ci gabansu.

Norway Oslo 2025 | Lambar Yabo ta Zaman Lafiya ta Nobel ga María Corina Machado | Ana Corina Sosa Machado
Norway Oslo 2025 | Lambar Yabo ta Zaman Lafiya ta Nobel ga María Corina Machado | Ana Corina Sosa MachadoHoto: Ole Berg-Rusten/NTB/AFP/Getty Images

Jagorar adawar Venezuela, Maria Corina Machado, wadda ta lashe kyautar Nobel ta Zaman Lafiya ta bana, ta ce dole kasashen da ke bin tsarin dimukuraɗiyya su shirya domin kare 'yancinsu, saboda ci gaban al'ummominsu.

Ta bayyana haka ne cikin wani jawabi da 'yarta, Ana Corina Sosa Machado, ta karanta a birnin Oslo, inda ta karbi lambar yabon a madadin mahaifiyarta wadda ba ta samu halarta ba.

Machado mai shekaru 58, ta ce wannan lambar yabo tana da muhimmanci ba ga kasarta kadai ba, har ma ga duniya baki daya, domin tana tunasar da duniyar cewa dimukuradiyya muhimmin ginshiƙi ne ga zaman lafiya.

Tun daga ranar 9 ga Janairun wannan shekarar, Maria Corina Machado  ba ta bayyana a bainal jama‘a ba, bayan da aka cafke ta na dan lokaci yayin da ta halarci wata zanga-zanga tare da magoya bayanta a Caracas babban birnin Venuzuela.