1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matar Trump ta jagoranci taron kwamitin sulhu na MDD

March 3, 2026

Melania Trump ta zama matar shugaban kasa ta farko da ta jagoranci zaman Kwamitin Sulhu na MDD. Ta mayar da hankali kan kananan yara, fasaha da ilimi a yankunan rikici, tana cewa ilimi ginshikin zaman lafiya ne.

Matar shugaban Amurka Melania Trump
Matar shugaban Amurka Melania TrumpHoto: Timothy A. Clary/AFP

A  taron da ta jagoranta a birnin New York a ranar Litinin ta bukaci a dauki matakai domin samar da zaman lafiya domin kyautata rayuwra kananan yara. Ta jagoranci taron a yayin da Amurka ta karbi shugabancin kwamitin daga watan nan na Maris. Taron ya mayar da hankali kan lafiyar kananan yara, fasahar zamani da ilimi a yankunan da ake fama da rikici.

Melania ta kuma jajanta wa iyalan wadanda suka rasa rayukansu a rikice-rikice, tana mai cewa Amurka na tare da yara a fadin duniya. Ta jaddada cewa ilimi na da muhimmanci wajen hana rikici da kuma gina zaman lafiya mai dorewa.

Sai dai ba ta yi tsokaci kan harin da Amurka da Isra'ila suka kai Iran da abin da ya biyo bayansa ba.