1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Matasa a Kenya sun kona majalisar dokokin kasar

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
June 25, 2024

Likitocin Kenya sun tabbatar mutuwar mutane 5 sakamakon arangama da 'yan sanda

Hoto: LUIS TATO/AFP

Dubban matasan da suka gudanar da zanga-zanga a Kenya sun kona majalisar dokokin kasar, bayan kutsa kai ciki, inda 'yan majalisar suka tsere, a daidai lokacin da suka amince da dokar karin haraji da shugaba William Ruto ya gabatar.

karin bayani:Arangama ta barke a Kenya tsakanin 'yan sanda da matasa

Sanarwar da kungiyar likitocin Kenya ta fitar, ta ce arangama da 'yan sanda suka yi da matasan ta janyo mutuwar mutane 5, bayan samun raunuka sakamakon harbin bindiga a Nairobi babban birnin kasar a Talatar nan. Haka zalika mutane 30 sun samu munanan raunuka.

karin bayani:Kenya: Kudurin doka na shirin haifar da rudani

Har ila yau masu zanga-zangar sun kona ofishin jam'iyya mai mulkin kasar da ke Embu a tsakiyar kasar.

Tun a makon da ya gabata ne daruruwan matasan suka fantsama kan titunan Nairobi, don nuna tirjiya da bijirewa wannan sabon tsari, da suka ce zai kara jefa al'ummar kasar cikin gararin rayuwa.