Matasa masu kishin Arewa a Najeriya
December 7, 2016Majalisar Daliban Najeriya ta Arewa dai kungiya ce da wasu matasa daga cikin jihohi 19 na Arewa ke shugabanta da nufin ganin suma ‘yayan talakawa ba a barsu a baya wajen samun ilmi mai nagarta ba. Kwamared Safwan Suraj Ilyas shi ne jagoransu a wannan tafiya, inda suka kai wa wasu makarantu tallafin da suke bukata a jihar Kano. A yanzu haka wannan tallafi ya game wasu daga cikin manyan makarantun yankin, wanda zai zama kari ne akan daukar nauyin kudaden jarrabawar kammala sakandire na wasu matasa da basu da sukuni.
Kwamared Suraj wanda ta kan dandalin sada zumunta da muhawara na Facebook ya fara ilmintar da matasa ya ce da su aka yi gwagwarmaya wajen sanya harshen Hausa a manhajar ta Facebook yana mai cewa su ma sauran ba zasu kyale su ba. Har yanzu kuwa dandalin na Facebook ne jagora da ‘yan Najeriya ke cin gajiyar abubuwa da dama na kafofin sadarwar zamani ciki kuwa har da bada ilmi ba tare da dalibi ya je aji ba. Matasa sama da 200 ne dai suka amfana da damar da wannan kungiya ta ma'abota hulda ta kafar sadarwa ta Facebook ke bayarwa, ta hanyar amfani da wadannan kafofin yada labarai da sadarwar fasahar zamani.