1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matasa sun kaucewa tarzoma lokacin zabe

Ibrahima Yakubu/Zainab Mohammed AbubakarMarch 31, 2015

Sarakunan gargajiya da malaman addinai da kungiyoyin sun yabawa matasa na kin amincewa tayar da zaune tsaye lokacin zaben shugaban kasa da senatoci

Wahl in Nigeria
Hoto: Getty Images/Afp


Ta koina a Najeriy, kungiyoyin fararen hula da malaman addinai tare da masu rike da mukaman gargajiya a cikin kasar, fitowa ne suka yi karara ta kafafen watsa labarai domin nuna jin dadin su ga irin jajircewa ga rawar da matasan kasar suka taka wajen kaucewa dukkanin hanyoyin da suka jibanci na karya dokokin zabe a ranar zaben da kuma yadda suka bada gagarumar gudunmawar tabbatar da ganin cewa sun kauce wa tayar da tarzoma lokacin zaben


Dr Auwal Abdullahi shi ne shugaban kungiyoyi masu zaman kansu a Kaduna da ke bayyana wasu daga cikin kokarin da suka yi na wayar da kan matasan da suka sami damar kaucewa fadawa cikin rikice-rikicen;

Ya ce "munyi murna matukar gaya da irin rawar da matasa, da malaman addinai da shugabannin 'yan siyasar kasar suka bada wajan samun zaman lafiya tun kamin zabe da lokacin zaben da kuma kokarin da suke yi na wajan ganin an sami bayan zaben. Babban burin da muke bukatar cimma anan dai shi ne na ganin an sami damar cimma burin amintaccen zabe, kuma duk abun da wadannan matasa ne bukatar gani shi ne na shawo kan matsalar da kasar ke cin karo da shi,domin samun hanyoyin ci-gaban kasa da alumma baki daya".

Suma dai masu rike da mukaman gargajiyan kasar yabawa matasan nigerian ne suka yi, kan yadda suka kwantar da hankalin su lokacin zaben da kuma yadda har yanzu suke ci-gaba da kokarin kawo zaman lafiya.

Hoto: Reuters/Afolabi Sotunde


Tuni su ma dai malaman addinai a kasar suka bi sahun sauran kungiyoyi da ke jinjinawa matasan gami da rawar da suka taka na kin amincewa tayar da kura a wannan lokaci kamar dai yadda Pastor Yohanna Buru na cocin Kirist Evengelical Fellowship ya nunar;

Ya ce "rawar da wadannan matasa suka taka,lallai dai kam abun yabawa ne,d omin kuwa wannan shi ne abun da ake nema, kuma abun mamaki a nan shi ne na yadda ba a sami rikici ko daya ba daga yankin Arewa sai dai a yankin kudancin kasar, a saboda haka muna ci-gaban da rokon al'ummar Najeriya da su ci-gaba da tabbatar da ganin cewa an sami zaman lafiya a cikin kasar".

Shi ma dai Alaramma Abdulrahman Mohamman Bichi ga abun da yake cewa;

Ya ce "wadannan nasarorin da muka samu, saboda da irin addu'o'i da sallolin da muka gudanar ne na samun dorewar dauwamanmiyar zaman lafiya a cikin kasar. Muna kuma rokon su na wajen ganin ko da an bayyana sakamakon zaben kada su tayar da hankali, maimakon haka su yi ta rokon Allah da ya kawo mana zaman lafiya".