1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matasa sun yi tir da rikici tsakanin majalisa da Buhari

Uwais Abubakar Idris
April 4, 2017

Dubban matasan Najeriya da ke da rajin kare dimokuradiyya sun yin zanga-zangar lumana zuwa majalisar dokokin kasar a Abuja don nuna bacin ransu a kan takadamar da ke tsakanin majalisar dattawa da fadar shugaban kasa,

Nigeria Proteste gegen Muhammadu Buhari in Lagos
Hoto: DW/S. Olukoya

Masu zanga-zangar sun ta rera wakoki suna cewa ba su yarda da halayen majalisar da ya haifar da takun saka tsakaninta da bangaren shugaban kasa ba. Batutuwan da matasan suka bayyana damuwarsu a kai sun hada da batun watsi da tantance mukadasshin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa, da fito na fito da suke yi da shugaban hukumar kwastom, har zuwa ga jingine amincewa da bukatar shugaban kasar .

Sai dai masu zanga-zangar da suka kai ga toshe daukacin hanyar shiga majalisar dokokin Najeriya sun fi rinjaya ne a kan batun dakatar da Sanata Ali Ndume, abin da ya sanya wasu takakka daga kudancin Borno zuwa majalisar, kamar Muhammad Alfa na kungiyar rajin kare dimokuradiyya .   

Buhari da saraki da Dogara sun gana don warware rikicin da ke tsakaninsuHoto: DW/U. Musa

Shugabannin majalisar dattawa sun aiko wakilai da suka yi wa masu zanga-zangar jawabi tare da alkawarin daukar matakai na maslaha da ma maido da Sanata Ali Ndume. Sanata Binta Masi Garba ce ta jagoranci 'yan majalisar.

Majalisar dattawan Najeriyar dai ta fara da zaman sirri, abin da ke sa jiran ganin matakin gaba da zata dauka a kan wadannan batutuwa bayan ganawar da shugabaninta suka yi da shugaban Najeriya a takadamar da ke daukar hankalin al'ummar Najeriya.