Tasirin kafar sada zumunta ga matasan Kenya
August 20, 2024
Kafar sadarwar Internet da ta zamo tamkar hanta da jini a rayuwar al'umar duniya a yau, fasaha ce da ta faro cikin shekarun 1960, inda a lokacin jami'an gwamnati ke musayar bayanai ta hanyar amfani da injuna masu kwakwalwa, sannan ake daukar ranar daya ga watan Janairun shekara ta 1983, a matsayin ranar kafuwarta a hukumance. Kafin samar da Internet a lokacin dai, kwamfutoci a duniya ba su da hanyar da suke iya aika wa juna da bayanai ko kuma musaya a tsakanin juna.
Karin Bayani: Babban sufeton 'yan sandan Kenya ya yi murabus
A shekara ta 1986 akwai sama da kwamfutoci dubu biyar da suke aiki da hanyar sadarwar internet. Adadin ya matukar karuwa zuwa miliyoyi a lokacin da manyan makarantu da masu harkokin kasuwanci suka rungumi fasahar sadarwar ta Internet. A shekarun 1990 Internet ta yi matukar yaduwa a fannoni dabam-dabam na duniya har ta kai halin da ake ciki a yanzu da a wasu kasashen masu bore da sauran nau'uka na zanga-zanga ke cin moriyar Internet fiye da yadda ake tunani.
Watanni biyu da suka gabata, duniya ta shaida gagarumar zanga-zangar adawa da gwamnati a kasar Kenya bayan aniyar samar da dokar sauye-sauye da ke da nasaba da kudaden haraji. Kungiyar matasa ta Zoomer Generation ko kuma Gen Z a takaice. Wasu dai na mai ra'ayin cewa abin da ya faru a Kenya, na kama da batu da ya samu goyon bayan wasu masu karfi daga gefe, walau na ‘yan adawa ko kuma kungiyoyi na kwadago.