1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Matasan Myammar sun fara arcewa don gudun aikin sojin tilas

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
February 26, 2024

Mahukuntan kasar sun farfado da dokar da ta tilastawa maza 'yan shekaru 18 zuwa 45 yin aikin soja na shekaru 2, mata kuma masu shekaru 18 zuwa 35 za su yi aikin

Hoto: AP

Matasan kasar Myammar sun fara tserewa daga kasar don kaucewa shiga aikin soja na tilas da sojojin da ke mulkin kasar suka assasa dokar yi.

Karin bayani:Myammar ta kakaba dokar tilasta wa matasan kasar aikin soja

A ranar 10 ga Fabarairun nan ne dai mahukuntan kasar suka sake farfado da dokar, wadda ta tilastawa maza 'yan shekaru 18 zuwa 45 yin aikin soja na shekaru 2, mata kuma masu shekaru 18 zuwa 35 za su yi aikin, wanda za a fara a cikin watan Afirilu mai zuwa.

Karin bayani:Aung San Suu Kyi ta kira Rohingya 'yan ta'adda

Kididdiga ta nuna cewa mutane miliyan 14 za su shiga aikin sojin, da suka hada da mata miliyan 7 da dubu dari bakwai, sai maza miliyan 6 da dubu dari uku, kamar yadda rundunar sojin kasar ta sanar. Duk wanda aka kama da laifin bijirewa wannan doka to zai fuskanci hukuncin dauri.