Matashi mai fafutukar yaki da shan miyyagun kwayoyi
September 14, 2016Talla
Abdubakar Sani Abdu wanda shi ma matashi ne ya ce babban burinsa shi ne taimaka wa dimbin matasa wadanda ya tabbatar babu yadda za su yi su taimaka wa rayuwar kansu, don haka yake iyaka yinsa na ganin suna rayuwa ta kwarai. Wannan shi ne abin da ya sa ya shiga wannan aiki na taimaka wa rayuwar matasan
Wannan matashi dan fafutukar dai tuni har ya kafa wata cibiyar tsugunar da matasa, kuma ya shaida wa wakilin DW cewar yakan yi bincike don gano inda matasan kan zauna su yi shaye-shaye, sa'anan sai ya tinkaresu da sunan zai yi abota da su kafin kuma a bisani sai ya bayyana manufarsa.