Matashi me sana'ar "POP" a Kaduna
June 5, 2019A jihar Kadunan Najeriya wani matashi da ya kammala karatun babbar difloma ta HND, ya kaurace wa rubuta takardun neman aikin gwamnati, inda a yanzu ya dukufa wurin amfani da iliminsa na kasuwanci wurin tallata sana’arsa ta “sanya ceiling na zamani, wato, P.O.P”. Abin da kawo yanzu ya ba shi damar mallakar kusan duk abin da matashi ke bukata. Sanusi Salisu a lokacin da yake ba da labarinsa mai cike da jarimta da himmatuwa ga neman halaliya. Sanusi ya ce tun yana karami ya fara koyon sanaa’ar sanya celing na zamani, wato, "POP" a gidaje, a saboda haka ya ce nasarorin da ya samu ba abin mamaki ba ne.
Jama’ar gari dai ba su san kalubale da matashin mai sana’ar sanya ceiling na "POP" ke fuskanta ba, abin da suke iya gani kawai shi ne nasarorin da ya cimma. Abin da ya sama ke nan Isah Abdullahi Ahmed, wani dattijo a garin Kaduna ke cewa koma dai Sanusi na fuskantar kalubale to ya cancanci a yaba masa.
Matashi Sanusi dai bai taba halartar wadansu kasashe ba, amma dai ya gamsu cewa karatun zamani abu ne da zai kara wa mutum fahimtar rayuwa da inganta kasuwanci ba wai dole sai an nemi aikin gwamnati da ilimin boko ba. A saboda haka ne yake cewa lokaci ya yi da sauran matasa 'yan Boko masu irin wannan ra'ayi za su nema wa kansu mafita domin kar mutum ya tsaya yana jiran aikin gwamnati har a zo lokacin da zai wa kan shi sakiyar da babu ruwa.