Matashi ya shake mahaifiyarsa har lahira
June 4, 2022A cewar ‘yan sandan, matashin mai suna Deepak ya shiga hannu a franar 3 ga watan Yuni bayan ya shake mahaifiyarsa Fathima Mary mai shekaru 50 a duniya har lahira a ranar 1 ga watan Yuni. ‘Yar’uwar matashin da ake tuhuma Joyce Mary ta shigar da kara ofishin 'yan sandan cewa masu bata gari ne suka kashe mahaifiyarsu a gonan lambunsu mai tazarar kilomita 5 kacal daga gidansu.
Deepak ya kira mahaifinsa Arogyaswamy ya gaya masa cewa mahaifiyarsa ta fadi a gefen hanya. Duk da haka, Deepak ya yarda cewa ya kashe mahaifiyarsa a cikin tambayoyin kamar yadda jaridar.
A cewar jami'ai, yayin da Fathima ke fita zuwa gona da safe, ta tunatar da Joyce cewa ta tura danta Deepak zuwa gona idan ya farka daga barci. Wajen azahar Deepak yaje ya dauko mahaifiyarsa, amma bayan wani lokaci ya dawo yace bai sameta a ko ina ba. Yayin da ’yan uwa ke neman Fathima, Joyce ta samu kira daga wayar mahaifiyarta da misalin karfe 2 na rana. Deepak da ke gefe ya shaida mata cewa mahaifiyarsu ta fadi a gefen titin, kuma ya yi zargin cewa wani ne ya shake ta.
'Yan sandan sun ce Deepak da isa gonar ya bukaci kudi n India rupee 20,000 daga wurin mahaifiyarsa Fathima domin ya siya wayar salula, amma ta ki ba shi kudin. Daga nan ya daka mata tsawa bayan ta mishi gorin cewa ba su biya mata bukata. don haka ba za ta iya bashi kudi don ya sayi waya ba.
Daga nan ne Deepak ya shake mahaifiyarsa har lahira sannan ya tsere da kudi rupee 700 dake cikin jakar mahaifiyarsa Fathima. Lokacin da ya isa gida, ya yi kamar bai san komai ba game da ita, in ji ’yan sanda. Daga baya, lokacin da aka tambaye shi, Deepak ya amsa laifin kamar yadda jaridar the Indian EPRESS ta ruwaito.