1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Injin barar gyada da surfen masara a Najeriya

August 12, 2020

A Najeriya wani matashin da ya kammala karatu ba tare da samun aiki ba ya rungumi sana'ar kere-keren kayayyakin noma da inganta rayuwar jama'a, kana wasu daga cikin nasarorinsa har da kera injinan barar gyada da masara

Gombe Recycling Machine

Matashin na daya daga cikin 'yan gudun hijirar da ke samun mafaka a Taraba "Nura mai walda" ya rungumi sana'ar kera kayayakin walda don dogaro da kansa. Wasu daga cikin nasarorin da yasamu har da na kera injimin barar gyada da masara da surfe a wani yunkuri na inganta harkokin noma da a Najeriya, kasar da mafi yawan al'ummarta ke dogaro da noman rani da damina don ci-gaban rayuwarsu ta yau da kullum.

Bayan kammala karatun boko ba tare da samun aikin yi ba, matashin ya rungumi sana'ar kere-kere da walda ne maganin zaman banza da kashe wando, kana kuma aikin ya taimaka masa sosai wajen kere-keren kofofin gidaje, sarrafa wasu karafan da ba'a amfani da su zuwa masu amfani, gyaran kayayyakin noman rani da damina tare da samar da fasahar gyaransu a wani mataki na tallafawa manoman da kuma kansa da kansa.

Burinsa shi ne ya ga an samu amfanin nom a da ingancin rayuwa ga 'yan Najeriya inda ya koyar da matasa da dama wannan fasahar ta kere-kere. Wasu daga cikin matasan sun nuna gamsuwa kan  yadda suke samun horo daga matashin Nura mai walda. Matashin ya yi kira ga 'yan uwansa matasa da su tashi haikan don bullo da hanyoyyin da za su kara bunkasa ci-gaban kasar Najeriya da iya fasahohin da Allah ya basu na rayuwa.