1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

HdM: Matashiya mai hada kayan lefe

January 12, 2022

Wata matashiya a Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno, na sana'ar hada kayan aure wato lefe, bayan kammala karatunta na jami'a.

Himma ddai Matasa | Maiduguri Najeriya
Matashiya mai sana'ar hadawa mutane kayan lefe a NajeriyaHoto: Al-Amin Suleiman Muhammad /DW

Matashiyar mai suna A'isha Muhammad Saje wacce aka fi sani da Aisha Saje tana sana'ar sayar da kayayyaki da su ka hadar da atamfa da da takalma da makamantansu, inda har ma ta samu nasarar bude shago. Sakamakon yadda matasa da ma wadanda suka manyanta ke neman a hada mu su kayan aure ko kayan lefe, ya sa matashiyar mayar da hankali wajen hada kayan gwagwaadon iko da karfin da mutum ke da shi. Wannan matashiya ta samu rufin asiri da wannan sana'ar, inda ta ce tana cire mata kitse a wuta.

Saidai kuma A'isha Saje ta ce, duk da tarin nasarorin da ta samu tana kuma gamuwa da kalubale a sana'ar tata. Masu Mu'amala da A'isha Saje suna yabawa kokarinta sosai, kamar yadda wasu daga cikinsu suka bayyana. Matashiyar dai ta dauki matasa irinta aiki, inda suma sana'ar ke taimaka musu a harkokinsu musamman ma na karatu baya ga wadanda yanzu haka suke koyon wannan sana'a a wajenta. A'isha Saje ta shawarci matasa da su nemi sana'o'in hannu, ta ce ta samun cikakken goyon baya da karfafa gwiwa daga iyayenta. A cewarta da hukumomi za su tallafawa matasa masu neman na kansu, za a rage matasa da ke zaman jiran samun aikin gwamnati wanda kuma ba samuwa ya ke yi ba.