1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arzikiAfirka

Matashiya ta rungumi sana'ar hada sabulai

November 17, 2021

Fati Halilou dai ta kansance matashiya ta farko a yankin Dosso da ke Jamhuriyar Nijar da take amfanni da ganyan itatatuwa dangin zogale, gabaruwa, zaitun da dai dangoginsu domin hada sabulai da man-shafawa kala-kala.

Seifenrindenbaum | Quillaria saponaria
Hoto: cc by Jason Hollinger 2.0

Fati Halilou matashiya a yankin Dosso da take amfanni da ganyan itatatuwa dangin su zogale, bagaruwa, zaitun da dai sauransu domin hada sabululuka da mayuka kala kala wadanda ke warkar da wasu cututuka kamar kaykayi da sauran cututukan fata. Lamarin da ya samu karbuwa ga al'umma duk da rashin tallafin da ke neman durkusar da sana'arta.

Warkar da wasu cutuka dai ta hanyar ganyen itatuwa wannan shi ne dalilin Fati Halidou ta fara hada ganyen itatatuwa gurin hada mayukan wanka da sabulai wanda ke warka da cututuka da dama na fata.

 A Jamhuriyar Nijar anfani da ganyen itatutuwa gun magance wasu cututuka dai ya kasance wata dadadiyar  al'ada wadda har yanzu  ke da daraja a gun wasu mutane. Mafi akasari dai mata ne aka sani wani lokaci har da maza ne suke kashe makuden kudade wajen sayen mai da kuma sabulai masu gyara fatar jiki, sai dai sannu a hankali wasu suka fara gane anfanin sabululuka da mayuka da aka hada da ganyen itatuwa.

A Jamhuriyar Niger dai galibi rishin tallafi daga hukumomi da kuma masu hannu da shini na taka muhimihar rawa gun durkusar da yan kanana kananan sana'oi.