1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arzikiAfirka

Matashiya ta rungumi sana'ar turaren wuta

April 28, 2021

A garin Maiduguri Zubaida Sani Ya'u wata matashiya bayan kamala karatun boko ta zabi yin sana'ar hada turaren wuta tare da sayar da shi a sassan Najeriya ta amfani da hanyoyin sadarwa na zamani.

BdT | Arabia: 19th century botanical painting of parts of a myrrh tree
Hoto: CPA Media Co. Ltd/picture alliance

 

Ita ce sana'ar hada turaren wuta da sauran kayan na jiki da na kamsasa daki ko wajen zama sana'a ce da ta shahara tsakanin al'ummar jihar Borno.

Sai dai ba kasafai ake samun masu karatun zamani su na yin wannan sana'a ba sabda yawanci an dauke ta kamar ta gargajiya ce ko ba ka yi don sayarwa ba ka yi don amfanin gida da sauran wuraren zama. Zabaida Sani Ya'u bayan kamala karatun ta na boko ta zamanantar da wannan sana'a ta hada turaren wuta da sauran kayan Kamshi na jiki wanda Amare da sauran matan Aure har da ‘yan mata ke amfani da su.

Wannnan matashiya ta shawarci sauran ‘yan uwan ta matasa da bayan sun yi karatu kada su tsaya neman aikin gwamnati maimakon haka su yi amfani da basirar wajen kirkirar sana'a da za su dogara da ita ta haka ne kawai za su cimma burin rayuwa.