Matsala ta kunno kai a jam'iyyar APC
June 9, 2013
An dai kaiwa ga zagaye gari har ma an fara kiran sunaye da nufin samar da sababbin shugabanni na riko ga sabuwar jam'iyyar adawar APC mai tashe da bada tsoro a cikin tarayyar Najeriya. To sai dai kuma ana shirin karya wa a cikin wani rikicin nadin na shugabanni a bangaren jam'iyyar da ta zauna ta kuma gaza kaiwa ga samar da shugabanni kamar yadda ta alkawarta.
Jam'iyyu kusan hudu da suka hadu su ka kai ga kyankyasar APC dai na fuskantar tasku ga wadda za ta samar da sabon shugaba da ma ragowar mukaman da a ke bukata domin mikasu ga hukumar zaben kasar ta INEC da ke da alhakin samar da rajista a gareta.
Tun da farko dai kwamitin da jam'iyyun su ka kafa domin tsara gamayyar dai ya tsara samar da shugaba ga ACN sannan da mataimakinsa ga ANPP. A yayin kuma da yar uwarta ta CPC zata fitar da sakataren riko ga APC. Matsayin kuma da ya bata ran yan ANPP da su ka ce ba za ta sabu ba, wai bindiga a ruwa .
ANPP da ke da gwamna uku a cikin hadakar dai a fadar majiyoyin taron da a ka kai ga gudanarwa a tsakanin Laraba zuwa daren Alhamis dai na tunanin samun abin da ya haura mataimaki domin daidaita tsarin da jam'iyyun ke ciki.
Abin kuma da ya tilasta mahalarta taron yanke hukuncin dakatar da nadin shugabanci da nufin kauce wa hayaniyar da ka iya aiko mugun sako a cikin Najeriyar da yanzu haka jam'iyyar ke ruruwa irin ta wutar daji.
Engineer Buba Galadima dai na zaman sakataren jamiyyar CPC na kasa, kuma a cewarsa bangarorin uku sun yanke hukuncin cigaba da amfani da shugabancin da ke kai yanzu, har zuwa ga samun rajistar da ke da matukar muhimmanci ga ayyukanta.
Sadaukar da kai domin ginin adawa ko kuma hadama ta rabon mukamai dai, babban kalubalen na zaman yanda za'a raba mukaman 'yan kwamitin zartarwa kusan 140 da kuma na kwamitin amintattu 90 a tsakanin A N P P da ke kallon tana da yawan shugabanni da kuma CPC dake kallon jama'a na goyon bayanta. Abin da ke zaman siradin farko ga jam'iyyar da ke da jan-aikin daidaita tsakanin 'ya'yanta a matakai daban-daban na gammayar , 'ya'yan kuma da kafin yanzu ba su kallon juna da mutunci.
To sai dai kuma a cewar Tijjani Musa Tumsah da ke zaman sakataren jam'iyyar ta ANPP na kasa, jam'iyyar ta su a shirye take domin karbar duk wani tsarin da yayi la'akari da karfi dama tasirin jam'iyyar a matakai daban-daban.
Abin jira a gani dai na zaman mafita ga jam'iyyun da baya ga batun na rabon mukamai ya kai ga tarwatsawa kawance da kuma yanzu haka ke tsakanin hadewa wuri guda da kuma ci gaba da jin ba dadi a hannun PDP da ta share shekara da shekaru tana basu ruwa.
Mawallafi : Ubale Musa
Edita : Saleh Umar Saleh