1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaSudan

Matsalar agaji ga mabukata a Sudan

Usman Shehu Usman
October 5, 2023

MDD ta koka da rashin tsaro da karancin kudi daga masu bada tallafi na kawo matukar cikas wajen isar da agaji ga miliyoyin 'yan Sudan wadanda yakin basasan kasar ya shafa.

Krieg in Sudan | Geflüchtete Grenze Tschad
Hoto: GUEIPEUR DENIS SASSOU/AFP

Babban jami'in ayyukan jinkai na MDD a Sudan Clementine Nkweta-Salami ya ce "muna bukatar isa ga mutane miliyan 18 da ke bukatar tallafin gaggawa, amma ba hali bisa karancin kudi da kuma rashin kariya ga ma'aikatanmu". Don haka ya yi kira da kasashen duniya su kawo karin dauki musamman kudi don a ceci al'ummar Sudan, ya yin da su kuwa masu yaki da juna ya nemi su bada sarari a kai ga mabukatan agaji.