1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Yara na fama da aikin karfi

Ramatu Garba Baba
June 10, 2021

Yara sama da miliyan 160 ake tilasta wa yin aikin karfi a fadin duniya inda annobar corona ta taka rawa a karuwar alkaluman inji Majalisar Dinkin Duniya.

Mosambik | Provinz Zambezia | Handwerklicher Edelsteinabbau
Hoto: Roberto Paquete/DW

A wani taro da suka gudanar a wannan Alhamis, Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Kwadago ta Duniya ILO gami da Asusun Kula da Yara Kanana na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, sun ce, alkaluman sun soma karuwa gabanin bullar annobar corona kafin matsalar ta kara ta'azzara, inda yanzu ake da yara sama da miliyan dari da sittin da ke aikin kwadago a sassan duniya.

Binciken da aka gabatar a gabanin ranar yaki da bautar yara ta duniya da Majalisar Dinkin Duniyan kan kebe a kowacce sha biyu ga watan Yuni, ya ce, kashi saba'in cikin dari na yaran na aikin karfi a gonaki, yayin da saura suka kasance a masana'antu da sauran aikace-aikace.

Taron yayi gargadi kan daukar mataki cikin gaggawa, a tallafawa iyaye da ke rayuwa hannu baka hannu kwarya, don ceto manyan goben daga kangin bauta, yara akalla miliyan hamsin ne ke fuskantar barazanar samun kansu cikin wannan matsala nan da shekaru biyu masu zuwa idan har aka kau da kai inji taron.