Matsalar cin hanci a kasar Laberiya
July 10, 2013Wani rahoto da kungiyar Transparency International dake yaki da almundahana da kudaden jama'a ta fitar, na nuni da cewa kasar laberiya ce ta biyu da ke da yawan mutanen da suke bada cin hanci da karbar rashawa. Gabanin wannan rahoto na Transparency International dai gwamnatin kasar ta sauke babban mai binciken kudi na kasar da kuma wasu shugabannin hukumomin gwamnati bisa zarginsu da laifukan da suke da nasaba da cin hanci da karbar rashawa. sai dai Shugaba Ellen Johnson-Sirlef na ci gaba da samun suka dangane da manufofinta na yaki da cin hanci a kasar.
Tun farkon darewarta kan karagar mulki a shekara ta 2006, Shugaba Ellen Johnson-Sirlef ta Laberiya ta sha alwashin yaki da cin hanci da karbar rashawa, to sai dai tuni ta fara samun suka daga bangarori daban-daban na kasar dangane da yadda take tafiyar da al'amuranta musamman a bangaren yaki da almundahana da kudaden jama'a. Shugaban hukumar yaki da halasta kudin haramun na kasar ta Laberiya (LACC) Cllr Frances Johson-Allison ya bayyana cewa Shugaba Sirlef na yin sassauci mai yawa ga masu halasta kudin haramun din.
Ya ce "Ni ina ganin shugabar kasa na son ta yi yaki da cin hanci da karbar rashawa, sai dai a kwai wasu abubuwa da dama da ke hanata yin yadda ya kamata, misali a kwai lokacin da ta amince cewa in tanaso ta kori ko kuma ta dakatar da wani da aka samu da laifin cin hanci daga kan mukaminsa, iyalai da abokan arziki sukan zo su roketa kan bai kamata tayi hakan ba. To ta na fuskantar kalubale da dama, amma in ka na so ka yaki cin hanci bai kamata ka zamo mai sassauci ba."
Sai dai kuma biyo bayan wannan batu na shugaban hukumar yaki da cin hanci na kasar ta Laberiya, Shugaba Ellen Johnson-Sirlef ta dauki matakin sallamar babban mai binciken kudi na kasar Robbert Kilby, a wani jawabi da ta gabatar tana mai cewa......:
Fara daukar tsattsauran mataki a kan masu almundahana a Laberiya
"A yau ina neman amincewar majalisar dokoki a kan sauke babban mai binciken kudi na kasa Robbert Kilby daga kan mukaminsa, bisa gazawarsa wajen bayyana harkokin kasuwancinsa da yake yi, wadanda kuma suke kawo cikas ga gudanar da ayyukansa na yin bincike da kuma ba da shawarwari a kan yadda za a tafiyar da dokokin kashe kudaden kasar."
Dangane da sukar da Shugaba Johnson-Sirlef ke ci gaba da fuskanta da ga al'ummar kasar, Mataimakin ministan yada labarai na Laberiyan Isaac Jackson, ya musanta zargin cewa gwamnati ba ta yin wani abun a zo a gani wajen yaki da cin hanci da karbar rashawa a kasar.
Gwamnati na kokarin kare kanta daga zargi.
Ya ce "Wadanda suke wannan zargi ba su da wata shaida da suka dogara da ita, a lokuta da dama ana sanya Laberiya a kan gaba wajen cin hanci da rashawa a duniya, kasancewar Laberiya a matsayin kasa ta uku da aka fi samun matsalar cin hanci ba wai ya na nuna mun gaza wajen yaki da wannan matsalar ba".
Duba da rahoton baya-bayan nan da kungiyar Transparency International ta fitar da ke nuni da cewa, a shekarar da ta gabata kawai kaso 74 cikin 100 na 'yan Laberiya ne ke bada cin hanci, tabbas za a ci gaba da dora ayar tambaya kan ko Laberiya ta samu nasara ko kuma akasin haka a yakin da take da cin hanci da karabar rashawa a kasar.
Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Saleh Umar Saleh