Matsalar fashin Teku a Somaliya
August 14, 2012Alƙalin wata kotun Amirka ya yanke hukuncin ɗaurin r ai-da-rai har sau 12 a gidan yari ga wani ɗan ƙasar Somaliya, bisa rawar daya taka a matsayin mai shiga tsakani domin samar da kuɗin fansar wani jirgin ruwan ɗaukar kaya mallakar Amirkar da 'yan fashin Teku a Somaliya suka yi garkuwa da shi a cikin watan Fabrairun shekara ta 2011. 'Yan fashin Tekun dai sun yi awon gaba da jirgin ruwan ne ɗauke da Amirkawa huɗu. Ɗaukacin Amirkawa huɗun ne dai 'yan fashin suka kashe duk kuwa da ƙoƙarin da sojojin Amirka suka yi na tattauna batun sakin su. A dai cikin watan Afrilu ne aka fara yankewa Mohammad Shibin hukunci bisa zarge-zarge 15 da aka same shi da aikatawa, waɗanda kuma suka haɗar da yin fashi a Teku, da yin garkuwa da jama'a domin samun kuɗi da kuma haɗin baki wajen aikata laifi. A cewar kotun dai an same shi da laifin karɓan kuɗin da yawan sa yakai dalar Amirka dubu 30 zuwa dubu 50 saboda aikin shiga tsakanin jami'an Amirka da kuma 'yan fashin da suka yi awon gaba da jirgin ruwan dama Amirkawan dake cikin sa.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Mohammad Nasir Awal