1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar Girka na ci gaba da girgiza kuɗin euro

September 26, 2011

Sakamakon rashin tabbas da ake ciki na ceto ƙasar Girka bisa rugujewar tallatalin arzikin ta, kasuwannin shunku a Turai na ci gaba da tangal-tangal

Ma'aikata a cibiyar kasuwar shunku dake Farnkfurt a kasar JamusHoto: dapd

A birnin Athens babban birnin ƙasar Girka ababen hawa sun tsa cik, sakamakon yajin aikin da ma'aikata ke yi. An samu cunkoso a birni na Athens biyo bayan tsaida aiki da ma'aikatan jiragen ƙasa da bas-bas waɗan da suka ƙaurawa cewa wuraren aikin na tsawon sa'o'i 24, inda suke adawa da shirin tsuke bakin aljihun gwamnati. Matakan stuke bakin aljihun da Giraka ke amfani da su, buƙatace da masu ba ta bashi na asusun bada lamuni na duniya wato IMF da kuma Tarayyar Turai suka shinfiɗa mata, muddin dai tana son ƙarin bashi a gaba. Masu bincike za su koma ƙasar Girka a makwan gobe domin dubu ko Girka tana bin sharuɗan kasafin kuɗi yadda aka tsara.

Tangal-tagal na kudin euro

Tsabar kwandololi na kudin euro kan tutar kasar GirkaHoto: picture alliance / ZB

Darajan kuɗin euro ya yi tangal tangal a buderwar kasuwanni shunku na yau, hakan bai rasa nasaba da shakkun da ake yi ko ƙasashen EU za su iya ceto ƙasar Girka mai fama da ɗimbin basuka. Takar dan kudin euro ta yi kasa idan aka kwatanta da dalar Amirka, kana euro ta samu koma baya kan kudin Yen na ƙasar Japan, wanda shine faduwa mafi girma tun shekaru 10 na baya. A halin da ake ciki dai jami'ai a ƙasashen da ke amfani da kudin euro suna kai kawo don ganin sun maido da darajar euro, domin kare tattalin arzikin ƙasashensu. A rahoton da jararidar Die Welt ta wallafa, ta rawaito ministan kuɗin Tarayyar Turai na cewa za su ƙara yawan kudin da suka ware don ajiya a asusun ko ta kwana. Ƙasashe 17 dake amfani da kudin euro sun amince da ɗaukar matakan bai ɗaya don dai- data tangal-tangal da harkar kudi ke yi a ƙasashensu. Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel tace ta na da gwarin gwiwa majalisar dokokin ƙasar za ta amince da tsarin da aka yi.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu