Matsalar karancin abinci a Sudan
January 5, 2012
Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa ta samu rahotanni dake bayyana tsanantar rashin abinci mai gina jiki ga al'ummar da ke kan iyakar kasar Sudan da suke tserewa tashin hankalin da ake yi, inda sojojin gwamnati ke yakar yan tawayen SPLM wani babban jami'in MDD yace al'ummar da ta tserewa fadar sun bayyana tsananin rashin abince da suke fiskanta, musamman a yankunan dake hannun yan tawayen SPLM. Tun a watan Juni fada ta barke tsakanin sojan gwamnatin Sudan ta kudu da yan tawayen SPLM a kudancin jahar Kordofan, kuma a yanzu ya yadu zuwa jihar Blue Niles. MDD ta yi kiyasin cewa mutane dubu 400 suka tsere daga gidajensu, kana fi ye da dubu 80, suka shiga Sudan ta kudu. Sudan ta kudu dai tun a watan Juli ta samu yancin kai, amma bata kai ga samun cikakken zaman lafiya ba.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Umaru Aliyu