1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar karancin man fetur na karuwa a Najeriya

Mansur Bala Bello/GATApril 29, 2016

Babu wani batu da ke daukar hankalin 'yan Najeriya kamar harkar farashin man fetur a kasar baya ga matsi da talakawa ke ciki sabili da matsalar a fannin tattalin arzikin kasa .

Benzin Afrika
Hoto: picture-alliance/ dpa

Jihar lagos mai dauke da akalla al'umma sama da miliyan 20 cike take da baki daga cikin gida da wajenta inda a wasu lokutan ake mata kirari da 'yar karamar Najeriya. Bincike dai ya nuna yadda masu ababan hawa sama da miliyan ne kan tituna a rana ta Allah, sai dai duk da wannan halin da ake ciki mazauna na fama da matsalar man fetur .

A waiwaye adon tafiya karamin Ministan man fetur na Najeriya ya tabbatar da cewa karancin man fetur ba ya rasa nasaba da zagon kasa da wasu ke yi na ficewa da man fetur zuwa kasashe makwabta kamar Kamaru da Chadi.

"Domin magance wannan magudin sai da gwamnati ta dauki matakli na soke wasu lasisin masu shiga da man fetur, amma kuma duk da haka kwangilar da ake bayarwa a baya, wasu ba su da wani tasiri. Sai dai don a sami kudi ba tare da gumi ba"

Hoto: DW

A Lagos, tuni gwamnati ta yi shelar dakatar da sayar da man a cikin Jarkoki domin a ganinta wata hanya ce ta tursasa wa talaka. Mista Idowu masani ne kan harkar da ta shafi sufuri a Najeriya:

"Mataki ne da wasu ke dauka na neman kudi cikin dare daya wanda dole ne gwamnati ta dauki mataki na ladabtar da duk wanda ke karar tsaye ga umarnin kasa"

Malam Ibrahim Jos matafiyi ne tsakanin Kudancin kasar zuwa Arewa ya ce abun takaici ne cewa duk da arzikin man fetur a Najeriya amma kwalliya na neman ta gaza a tsakanin 'yan kasar:

Hoto: dapd

"A lokuta da dama ana sayar da lita daya Naira 150 maimakon 87 a gaskiya mazauna Lagos na cikin kuncin zama" .

Mista John KK na ra'ayinsa cewa ya yi wata makarkashiya daga masu sayar da man fetur din a gidajen mai:

"Matsalar ba daga gwamnati take ba illa daga wajen masu gidajen mai ne da suke sayar da man a cikin tsakar dare wanda a nufinsu shi ne sai gwamnati ta kara farashin man fetur domin cigaba da yadda ake baya".

Bincike da DW ta gudanar ya nuna cewa a wasu gidajen man fetur din akwai mai sai dai dogon layi wanda ba shi misaltuwa.

Wata kididdiga ta nuna cewa akalla ana samun motoci sama da miliyan daya akan titunan lagos amma sabili da rashin man fetur kalilan ne ke kan tituna

Farashin kayan masarufi da na kyale-kyale duka ya tashi sabili da rashin fetur a birnin na lagos

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani