1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karancin wutar lantarki a Najeriya da Nijar

April 18, 2019

Duk da cewar yanayi na zafi ya dauki sawu a yawancin kasashen Afirka da ke yankin kudu da Sahara, matsalar klarancin wutar lantari na ci gaba da damun jama'a musamman masu sanao'i.

Afrika Elektrizität Nigeria Afam VI
Hoto: Getty Images/AFP/F. Plaucheur

Wannan matsalar daukewar wutar lantarkin dai ta saka  al'umma cikin tarin matsaloli game da al'amuran rayuwarsu ta yau da kullum inda har jama'a suka fara kwana a bakin panpuna wajen neman ruwa.

Tuni dai jama'a suka fara bayyana fargabarsu da wannan matsala game da yadda zasu kasance tare da ita  a cikin watan azumin Ramadan.


Wannan matsala ta karancin ruwa ta fara tsamari ne kamar yadda wasu daga cikin mazauna unguwannin kan tudu suka koka. Inda suke kwashe fiye da rabin sao'in dare ba tare da ko iska ta zo a pampunan su ba matsalar da a cewar su a shekarun baya hukumomi ke daukan ta a zaman tarifi a wanan birni da kewaye


A yanzu haka dai al'ummar birnin na Damagaram ta haura a ganga dubu 24 inda kuma a kan samu tarin jarkoki a pompunan kan layi a wurare daban daban, da suke shiga layi ko da ruwa yazo cikin dare yayin da wasu unguwannin basu ma san da ko ana wuyar ruwa ba.