1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan Afirka na da matsalar samun bizar Jamus

Daniel Pelz | Gianna-Carina Grün MNA
June 7, 2018

'Yan Afirka da ke gabatar da bukatun neman bizar shigowa Jamus a ofisoshin jakadancin Jamus da ke ketare, na fuskantar babban kalubale wajen samun bizar.

Afrikanischer Reisepass
Hoto: picture-alliance/Godong

'Yan Afirka da ke gabatar da bukatun neman bizar shigowa Jamus a ofisoshin jakadancin Jamus da ke ketare, na fuskantar babban kalubale wajen samun bizar. Wani bincike na bayanai da tashar DW ta yi, ya nuna cewa ana watsi da kashi daya bisa biyar na bukatun neman biza a Afirka, adadin da ya zarce fiye da kima idan aka kwatanta da na masu neman bizar shigowa Jamus din daga wasu nahiyoyi. 

Grace Boateng 'yar kasar Ghana ce da aka canja sunanta, ta yi tsammanin samun biza cikin sauki. Shekaru uku da suka wuce lokacin da 'yar shekaru 26 da haihuwa ta gabatar da takardar neman biza a karon farko a ofishin jakadancin Jamus da ke birnin Accra, an yi watsi da bukatar, bisa hujjar cewa ba tabbas za ta koma gida Ghana bayan bizar ta kare, duk da a cewarta ta cike dukkan ka'idojin neman bizar.

Sau uku ta mika bukatar ana watsi da ita, sai a karo na hudu bukatarta ta biya. A hira da DW Grace Boateng ta ce ta yi imani asalinta ne babban dalilin hana ta bizar da farko.


"Me ya sa al'ummomi daga wasu kasashen ke samun saukin zuwa Jamus amma 'yan Afirka sai sun sha da kyar. Mene ne bambamci tsakanin wanda ya fito daga China ko Austreliya? Dukkanmu 'yan Adam ne, kudin biza daidai muke biya, muna cike ka'idoji iri daya da kuke nema."

Shin zargin da ta yi haka ne kuwa? A wani bincike na bayanai yadda ake ba da biza a ofisoshin jakadancin Jamus daga 2014 zuwa 2017 da 'yan jaridar DW suka yi, sun duba bukatar neman biza ta dogon lokaci don neman karin ilimi a Jamus da aiki da zama tare da iyali, amma ba su binciki ta gajeren lokaci ba.

Tsakanin 2014 zuwa 2017 yawan bukatun neman bizar a ofisoshin jakadancin Jamus ya karu da kashi 58 cikin 100, yayin da wanda aka yi watsi da su suka kai kashi 131 cikin 100. A tsukin wannan lokaci kashi 10 cikin 100 ne kadai daga Afirka aka yanke shawara a kai. Mafi yawa daga Asiya ne da kashi 60 cikin 100, da kasashen Turai wadanda ba na EU ba da suke da kaso 23 cikin 100. Daga cikin wadanda aka yi watsi da su Afirka ce a sahun gaba da kashi 22 cikin 100 wato daya bisa biyar, Turai daya bisa takwas sannan Asiya daya bisa 10.


Ma'aikatar harkokin wajen Jamus ta ki amsa bukatar DW don yi hira da ita kan sakamakon bincike, illa iyaka ta sanar da DW cewa kowane ofishin jakadanci na da ikon yanke hukunci da kanshi kan batun na ba da biza.
Jochen Oltmer manazarci ne a harkokin da suka shafi kaura a jami'ar birnin Osnabrück da ya ce ko shakka babu asalin kasa na taka rawa.

 

"A kullum ana duba yanayin siyasar cikin gida na kasar da mai neman bizar ya fito. Idan akwai barazana ta tsaro ko kiwon lafiya ko rashin kyakkyawan tsarin zamantakewa a kasa, shin kasa ce mai bin doka ko a'a. Jamusawa na wa Afirka kallon nahiya mai fama da talauci da yawan masu son yin kaura. Saboda haka ana yi wa mai neman biza daga nahiya kallon wanda zai shigo Jamus don cimma wasu bukatun daban da wadanda ya gabatar wajen neman biza."

Watakila wadannan su ne dalilan da za a iya cewa ke bayanin abin da ya sa aka samu babban bambanci na yawan bukatun neman bizar da aka yi watsi da su tsakanin kasashe dabam-dabam. Alkalumman sun saba wa ikirarin gwamnatin Jamus na saukaka wa matasan Afirka hanyoyin shigowa Jamus, musamman don neman karin ilimi ko koyan sana'a.