1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya na fuskantar hadari na sauyin yanayi

Uwais Abubakar Idris AH
November 6, 2023

Najeriya cibiyar hasashe da tsara manufofi ta Agora da hadin guiwar kungiyoyin kasa da kasa ta fitar da wani rahoto da ya nuna hatsarin da ke fusknatar Najeriya sakamakon sauyin yanayi.

Hoto: Katrin Gänsler/DW

Wannan rahoto da ya yi nazarimai zurfi a kan wannan matsala ta sauyin yanayi a Najeriyar da ke kara bayyana a fili musamman  canji na bazata daga yanayin da aka saba da da shi. Kama daga ambaliya ruwa zuwa gurgusowar hamada da fari. A 'yan kwanakin nan ana yanayin rani haka katsam sai ruwan sama da ya lalata amfani gona mai yawa. Waziri Adio shi ne shugaban cibiyar ta Agora ya shaida mana abubuwan da suka gano da suka tayar masu da hankali.‘’Ya ce: sauyin yanayi ya haifar ma da barazana mai yawa a matsayinmu na kasa, albarkatun gona da ake samu na ci gaba da raguwa wannan ya haifar da zaman tankiya a tsakanin alummu musamman tsakanin makiya da manoma, a yankin Niger Delta da jihar Benue duka sauyin yanayi ya haifar da matsala. A wadannan wurare mun ga yadda rigingimu ke faru a dalilin wannan matsala’an yi karin kasafin kudin Najeriya’.

Barazanar yunwa sakamakon sauyin yanayi za ta shafi al'uumma a Najeriya

Hoto: DW

Wannan ne dai karon farko da wata cibiya ta zauna a tsanake ta fitara da rahoto tare da tsara manufarta da take son ganin an dauka a hukumance a kan matsalar. Najeriyar da ke a yankin kasashen Sahel ta kasance cikin wadanda ke fuskantar matsalar  ta karancin abinci da ma barazanar da yunwa ke yi, wacce hukumar abinci da aikin gona ta ce za ta shafi mutane milyan 25 a wannan shekarar,duka saboda matsaloli na sauyin yanayi da ma rashin tsaro.Gwamnatin Najeriyar dai ta sanya hannu a kan yarjeniyoyi iri dabam-dabam na kare muhalli to sai dai babu wani sauyi da ake samau na zahiri. Shin me gwamnatin ke yi a hanzu da cibiyar ta Agora ta fitar da wannan rahoton.Mohammed Idris ministan yada labaru da wayar da kan jama’a na Najeriya ya ce suna dauikar matakai. Cibiyar ta Agora ta bayyana abin da take ganin mafita daga wannan matsala. Kwarraru na bayyana cewar daukan matakan da suka dace a kan lokaci muhimmi ne domin sauyin yanayi dai zahiri ne kuma yana ci gaba da barazana ga rayuwar bani Adama.

Hoto: Fatai Campbell/AP Photo/picture alliance
Hoto: DW