Matsalar sufuri tsakanin Nijar da Burkina
July 28, 2022Babbar kungiyar ‘yan Nijar masu kasuwancin kasa da kasa ta nuna damuwa dangane da yadda daruruwan motocin kasar dauke da kayan abinci suka makale watanni da dama a Burkina Faso a sakamakon yadda matsalar tsaro ta yi kamari kan hanyar da ta hada kasashen biyu. Moussa Tchambiano babban sakataren kungiyar ya ce: " Motocin sun kai watanni biyu a tsaye kuma yawansu ya kai 300 ko ma zuwa sama. Sun zo a garin Fada Ngourma suka tsaya, domin tsakanin wannan gari da Kantchari, da ma zuwa cikin Nijar akwai 'yan ta'adda. Suna tsayawa su binciki lafiyar hanya kafin su taho. To amma yau sama da mako daya, wasu sun iso, wasu kuma babu labarinsu."
Ita kuwa kungiyar direbobin manyan motocin jigilar kaya wadanda su ne abin ya fi shafa kai tsaye ta nuna damuwa a game da halin da 'ya'yan kungiyar ta ke ciki a kan hanyar. Mahamadou Gamatche,shugaban kungiyar kwadagon direbobi ta UTTAN ya ce: "Lallai abokanmu durobobinmu na Nijar suna cikin tsaka mai wuya, domin tun lokacin da 'yan ta'adda suka fara tare manyan motoci masu dauke da abinci ko man fetur, aikin namu ya shiga wahala...Suna tsoron ‘yan ta'addan su kama su, su gallaza masu."
Kungiyar manyan 'yan kasuwan ta yi kira ga gwamnatocin kasashen Nijar da Burkina da su samar da rundunar hadin gwiwa wacce za ta dinga rakiyar motoci kan hanyoyin kasashen biyu. Ya ce:"Nijar da Burkina Faso su hada kai su samar da rundunar hadin gwiwa ta sojoji... Idan ba su yi haka ba , mu ba mu da wata dabara. Kuma fargaba ita ce yankewar kayan abinci a nan gaba, domin wannan hanya kasashe biyar ne ke amfani da ita wato Togo da Ghana da Nijar da Mali da Côte d'ivoire””
Sau tari kungiyoyin 'yan ta'adda sun yi awon gaba da motocin abinci da na man fetur a kan wannan hanya wacce ta hada kasar ta Nijar da Burkina inda sannu a hankali lamarin tafiye-tafiye ke kara zama babban hadari.