Matsalar tsaro da rikice-rikicen siyasa sun zafafa a duniya
Umaru AliyuNovember 26, 2015
Kasashen Mali da Tunisiya da Nijar da wasu na Turai na fama da hare-haren 'yan tarzoma, yayin da Turkiya ta fara rikici da Rasha bayan da ta kakkabo jirginta a kan iyaka.
Talla
Mali da Tunisiya da Nijar da Kamaru da Faransa sun samu kansu cikin wadi na tsaka mai wuya sakamakon hare-haren ta'addanci. Ita kuwa Turkiya ta fara takun saka da Rasha bayan da ta kakkabo mata jirgin sama.