Matsalar tsaro na barazana ga aikin jarida
May 3, 2019A yankin arewacin Najeriya musamman jihohin Zamfara da Kaduna da Katsina da sauransu lamuran tabarbarewar tsaro na kawo cikas ga aikin jarida a jihohin ganin yadda ‘yan jaridar basu da damar gudanar da aikinsu cikin kwanciyar hankali. Wannan ya sanya da dama manema labarai suka dena shiga yankunan karkara don gudanar da aikinsu.
Kasancewar garkuwa da mutane ta yi yawa a kauyika da yankunan da ke zama dazuka, su kuma al'umma na tsoron tattaunawa da 'yan jarida musamman a yankunan na karkara.
An dai ga yadda aka rika kama 'yan jarida ana garkuwa da su a Najeriya, ga misali an kama dan jaridar gidan rediyon Muryar Amirka da na gidan talabijin na kasa a Najeriyar. Wasu 'yan jaridar sai da aka biya makudan kudade na fansa kafin a sake su. Wannan na zuwa baya ga kalubale da suke fuskanta a bangaren jami'an tsaro da ma na gwamnati.
Kungiyoyin 'yan fafutika dai a Najeriyar na son ganin an ba wa 'yan jaridar kariya ta yadda za su rika gudanar da aikinsu yadda ya kamata.