1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar tsaro na jan hankalin dattawan Najeriya

Ubale MusaNovember 4, 2014

Majalisar zartarwar Najeriya ta nuna bakin ciki sosai dangane da yadda lamuran tsaron kasar suka tabarbare kuma sun bukaci gwamnati ta yi gyara cikin gaggawa

Nigeria Abuja Nationalrat
Hoto: DW/U. Musa

Kama daga batun rashin tsaro da ma siyasar dake tinkarar tarrayar Najeriya dai sun share tsawon wunin Talata suna nazarin halin da kasar take ciki ga 'ya'yan majalisar koli ta dattawan Najeriya da ta kammala taron ta yammacin yau a Abuja.

Abun kuma da ya dauki hankalin dattawan kasar ta Najeriya da suka share wunin yau suka kuma shaida wa gwamnatin tana bukatar tashi a tsaye da nufin kai karshen matsalar kafun zabukan kasar dake tafe. A fadar Dr Babangida Aliyu dake zaman gwamnan jihar Nijer kuma a cikin mahalarta taron.

“ kasan dama yakin sunkuru yanda yake to amma tun da yanzu sun fito dara dara har suna kama garuruwa to dole ne mu tunkare su kuma gwamnati tayi alkawin karin karfi”

Hare-hare sun yi yawaHoto: picture-alliance/dpa

Matsalar tsaron Najeriya ta wuce gona da iri

Shawarar ta dattawan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da ayyuka na kungiyar na kara ta'azzara dama kame garururwa daban-daban cikin sashen na arewa maso gabas. To sai dai kuma a fadar Air Chief Marshal Alex Badeh dake jagorantar kasar cikin yakin dai wai ta kai ga yi musu duhu dama baki ga yanda yakin ke tafiya ya zuwa yanzu

“Ya Najeriya za ta kasa, ai ba za ta yiwu maganar na rasa gari na daya ne da rasa Legas ko Enugu duk daya ne in wani bangaren Najeriya ya tafi. saboda haka in a rasa gari na ko an kona gida na ko na Emeka dole ne in ji ciwo”

To sai dai kuma ko bayan barazanar rashin tsaron dai majalisar ta kai ga amincewa da nadin babban sufeton 'yan sandan kasar cikin rudu na siysar son kai. A cikin makon jiya ne dai Suleman Abba ya bada umarnin janye jami'an tsaro na 'yan sanda daga shugaban majalisar wakilan kasar Aminu Waziri Tambuwal, kafin daga baya a a yau ya kai ga samun sakaiyyar ta amincewa.