1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Matsalar tsaro na kamari a yankin Sahel

October 5, 2023

Kasashe uku na yankin Sahel da ke karkashin mulkin sojoji da suka hadar da Mali da BurkinaFaso da Nijar na ci gaba da fuskantar munanan hare-haren ta'addanci,

Niger | Demonstration von Putschisten in
Hoto: Balima Boureima/picture alliance/AA

A 'yan kwanakin nan barazanar 'yan ta'addar na kara ta'azzara lamarin da ke dasa ayar tambaya kan alkawarin da sojojin suka yi na murkushe 'yan ta'addar ba tare da tallafin kasashen waje ba.

Kasashen uku masu makwabtaka da juna da suka hada da Mali da Burkina Faso da Nijar sun yanke shawarar kafa sabon kawancen mai lakabi ''Kwancen tsaro na yankin Liptako Gourma'' bayan da suka raba gari da kasar Faransa wacce suka kwashe shekaru da dama suna damawa da ita a fannin tsaro da kuma yaki da ta'addacin. To sai dai kusan watan guda bayan yanke kawacen, har yanzu kasashen sun kasa tabuka komai a game da matsalar wace hasali ma ke kara dagulewa a kan iyakokinsu.

Yaki da mayakan Jihadi a yankin SahelHoto: Inside the Resistance

A baya-baya nan kungiyoyin 'yan ta'adda sun halaka sojojin Nijar 26 a kan iyakar kasar da Mali mai makwabtaka. Wannan hari dai na zama mafi muni da aka kai wa sojojin Nijar tun bayan hawan sojoji kan madafun ikon wandanda suka kafa hujja da dagulewar matsalar domin hambarar da gwamnatin farar hula ta Mohamed Bazoum a ranar 26 ga watan Yuli. Abassa Zirdine wani mazauni garin Anzourou da ke yankin Tillabery na Yammacin Nijar ya shedar da cewa watanni biyu bayan zuwan sojoji kan madafun iko babu abin da ya canja a game da matsalar tsaro a yankin, hasali ma cewa ya yi lamura kara dagulewa suke yi a yankin.

''Al'amarin tsaro na kara sukurkucewa a yammacin jamhuriyar Nijar. 'Yan ta'adda sun ninka hare-haren da suka saba kai wa sojoji da fararen hula. Hakan kuma ya kawo nakasou ga tafiyar da ayyukan jinkai a wannan yaki''.

Yaki da mayakan Jihadi a yankin SahelHoto: Inside the Resistance

Baya ga Nijar, a Burkina Faso ma duk kanwar ja ce, domin murkushe 'yan ta'adda da gwamnatin kyaftin Ibrahim Traore ta alkawarta ya ci tura. Hasali ma, yawaitar hare-haren masu da'awa da makamai ya kai gwamnatin mulkin sojan daukar matakin rufe cibiyoyin harkar ma'adinan zinare da ke Gabashin kasar inda 'yan ta'addar suka cika ka hari. A cewar Serge Zongo wani da ke aikin hako zinari, 'yan ta'addar na son kame cibiyoyin harkar karfen mai daraja damin samun kudaden tafiyar da harkokinsu.

"Yau da gobe aikin hakar zinare ta zama hanyar samar wa 'yan ta'adda da kudaden shiga, kuma wannan harka na zama silar karuwar kashe-kashen da ake wa al'umma.''

Daga bangare ta kuwa Mali, baya ga matsalar 'yan ta'adda da ke gwagwarmaya da makamai yau da 'yan shekaru a Arewancin kasar, wani sabon kalubale da ke gaban gwamnatin ta kanal Assimi Goita shine batun 'yan tawayen Abzinawa na yankin Azawad masu fafutukar raba kasar gida biyu da suka sake kunno kai, inda suke matsa lamba a yankin Kidal bayan sun yi watsi da yarjejeniyar Algies.

A yanzu haka dai Arewacin na Mali na cikin hali na gaba kura baya sayaki bayan fadawasa cikin tarkon 'yan tawaye da kungiyoyin jihadi masu alaka da IS wadanda bayan sun yi garkuwa da birnin Timbuktu ke neman karbe iko da birnin Meneka. Houseini Ag Yehiya wani mazaunin birnin Meneka, ya shadar da cewa wannan lamari ya tilasta wa darurruwan mutane fara tserewa daga yankin.

Yaki da mayakan Jihadi a yankin SahelHoto: Inside the Resistance

Dama birnin Meneka ya fuskanci tashe-tashen hankula na kungiyar IS musamman ma kan iyakokin Mali da Nijar, lamarin da ya tilasta wa al'umma tserewa zuwa Meneka. A halin garin Meneka kadai ya tsira daga fada wa hannu wadannan kungiyoyi, to idan har kuma 'yan tawayen Abzinawa suka sake daukar makamai to ba shakka wannan wani sabon kalubalen tsaro ne ga Mali.

A Mali dai tun bayan ficewar sojojin Faransa da kuma dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya MINUSMA daga kasar a baya-bayan nan, kungiyoyi 'yan ta'adda da suka yi likimo na dan lokaci suka sake farfadowa tare da zafafa hare-hare a Arewacin kasar. Sannan a hannu guda kuma sake dawowar 'yan tawayen Abzinawa na Azawad na iya kara karfin 'yan ta'addar lamarin da ake gani ba shakka zai dagulawa lissafi gwamnatin kasar.