1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalolin kasuwancin litattafai anahiyar Afirka.

YAHAYA AHMEDNovember 7, 2005

Shirin na yau zai dubi matsalolin da ake huskanta ne a fannin dab’i ko kuma buga litattafai da kasuwancinsu a nahiyar Afirka. A karshen makon da ya gabata ne aka kammala taron baje kolin litattafan nan na kasa da kasa, mafi kasaita a duniya, wanda ake gudanarwa a ko wace shekara a birnin Farnkfurt na nan Jamus.

Alamar kasuwar baje kolin litattafai ta Frankfurt ta wannan shekarar.
Alamar kasuwar baje kolin litattafai ta Frankfurt ta wannan shekarar.

Kamar dai a shekarun da suka wuce, bana ma masu kula da tsara shirye-shiryen taron sun ce, an sami bunkasar masu baje kolin da kuma mahalarta kasuwar. Amma a bangare daya kuma, tun kusan shekaru biyar dai ke nan a jere da ake ta kara samun ragowar mahalarta wannan gagarumin bikin daga nahiyar Afirka. `Yan kasashen nahiyar kadan ma da suka iya zuwa, sun yi hakan ne tare da taimakon raya kasashe da ta samu daga gwamnatin Jamus, karkashin wata yarjejeniya ta musamman.

A zahiri dai, kasashen na Afirka na huskantar mattsaloli iri-iri a halin yanzu, musamman na tattalin arziki. Sabili da haka ne kuwa, kasashe da dama ke gaza turo wakilansu, idan suka yi la’akari da hauhawar farashin rumfuna a zaurukan nunin da kuma na masauki a lokacin bikin. Har ila yau dai, kasuwancin litattafan ma na huskantar koma baya a nahiyar.

Da can dai a kan gudanad da wani taron baje kolin litattafai na kasashen nahiyar a ko wace shekara a birnin Harare na kasar Zimbabwe. To, a nan ma saboda matsaloli da dama, musamman ma dai na siyasa, tare da matsin lambar da kasashen yamma ke yi wa gwamnatin shugaba Robert Mugabe, taron na samun koma baya. Bugu da kari kuma, kafofin kasashen ketare da ke halartar taron suke kuma taimaka wa gwamnatin kasar wajen shirya taron, sun janye tallafin da suke bayarwa. Ita kadai kuma, wato kasar Zimbabwen, a halin da ake ciki yanzu dai, ba za ta iya daukar nauyin ci gaba da gudanad da taron ba.

A gun taron birnin Frankfurt dai, an yi muhawara a kan wannan batun, a dandalin kasa da kasa da aka kebe musamman, don tattauna batutuwan da suka shafi matsalolin dab’i a kasashe masu tasowa. Hukumar kula da tsara shirye-shiryen taron baje kolin na Frankfurt ta ce, an kammala wani shiri tsakaninta da kungiyar `yan kasuwar litattafai ta kasar Afirka Ta Kudu da kuma gwamnatin wannan kasa, don bude wata sabuwar kasuwar baje kolin litattafai na nahiyar Afirkan a birnin Cape Town. A cikin watan Yulin shekara mai zuwa ne dai, ake sa ran gudanad da wannan taron.

To ko wannan shirin zai iya farfado da kasuwar litattafai da kuma sha’awar bunkasa adabi a nahiyar ? Ana dai kyautata zaton haka. Amma kafin a iya yin wani ikirari, sai an ga irin sakamakon da taron na Cape Town zai haifar, a shekarar badi.

To wannan ke nan.

Harshen Hausa na daya daga cikin muhimman harsunan Afirka da suka fi yaduwa zuwa kasashen ketare, nesa da inda suke da asali. Haka kuma al’adun su Hausawan da kansu. Ana iya ganin hakan ne dai, musamman idan a nufi Gabas, zuwa kasashen Larabawa kamarsu Sudan da Saudiyya.

Wakilinmu, Salisu El-Mansur, wanda a halin yanzu haka, yake kasar Saudiyya, ya bi diddigin wannan batun, don samo mana karin bayani game da yadda harshen Hausan ya kankama a wadannan kasashen da kuma yadda Hausawan ke tafiyar da al’adunsu. Wai shin, Hausawan da suke zaune a wadannan yankunan kawai ne ke amfani da harshen Hausan ko dai harshen da kuma al’adun Hausawan ya yadu ya kuma sami karbuwa ga sauran al’ummomi da ke zaune a can ?