1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

240908 Finanzkrise China

Gui, Hao (DW China) September 24, 2008

Matsalolin tattalin arziki dake ci-gaba da na ƙara ɗaukar kannu labaru a duniya baki ɗaya. Yanzu haka dai wannan matsala ta cimma kasuwannin hada-hadar kuɗi a ƙasashen nahiyar Asiya.

Kasuwar hada-hadar hannayen jariHoto: AP

To sai dai China wadda ke kan gaba wajen samun bunƙasar tattalain arziki a Asiya wadda kuma har wayau ta ke ɗaya daga jerin ƙasashen da suka fi bawa Amirka bashi ta na ɗari-ɗari wajen ɗaukar matakan kare kasuwanninta.

Tun ba yau ba tattalin arzikin ƙasashen Amirka da China sun sha faɗi tashi tare. Hulɗoɗin cinikaiya tsakaninsu na tafiya ne ƙarƙashin wani tsari na ba ni gishiri in ba ka manda. In ban da tarayyar Turai da Japan Amirka ce a matsayin na uku tsakanin ƙasashen da suka fi tafiyar da hulɗar cinikaiya da China. Ƙasashen biyu suna ba juna cikakken haɗin kai a fannin hada-hadar kuɗi, inji Markus Taube Farfesa na harsunan al´umar China a jami´ar Duisburg. Ya ce wannan dangantaka ta ƙut da ƙut ta fi fitowa fili a wannan lokaci na matsalolin tattalin arziki.

Ya ce: "Bankunan zuba jari na Amirka sun shiga cikin harkokin banki a China ƙwarai da gaske. Wato abin nufin tsarin kafa irin waɗannan bankuna a China daidai yake 100 bisa 100 da na Amirka. Shi ya sa idan bankunan Amirka da na Chinan ke koyi da su suka durƙushe to haka zai tasiri a kasuwannin China. Shi ya san ayar tambaya a nan ita ce shin ba kuskure ba wajen koyi da tsarin bankunan Amirka?. Kuma wani mataki ya kamata a ɗauka nan gaba?"

A wani matakin farko na ba zata da babban bankin China ya ɗauka na rage kuɗin ruwa don bawa bankunan ƙasar wata sa´ida. Bugu da ƙari gwamnati ta saye hannayen jari masu yawa daga bankuna don ceto sdu daga tsunduma cikin matsala. Ko da yake wannan matakin gaggawan zai taimaka a farfaɗo da hada-hada a kasuwannin cinikin hannayen jari na gajeren lokaci amma ba zai tasiri na dogon lokaci ba, inji Frank Tian Xie Farfesa a fannin harkar kasuwanci na jami´ar Drexel dake Amirka.

Ya ce: "Matsalolin kuɗi a Amirka zai janyo tafiyar hawainiya wajen samun bunƙasar tattalin arziki. Hakan ya shafi harkar fid da kayan China zuwa ƙetare wadda ta dogara sosai akan kasuwannin Amirka. Ko da yake ba a ganin tasirin yanzu amma nan da makonni ko watanni zai kunno kai."

Kawo yanzu matsaloli a kasuwannin hada-hadar kuɗi a duniya baki ɗaya ba su shafi China dangane da matakan daidaita kasuwanni da take ɗauka da kanta. Duk da cewa an samu faɗuwar maki a kasuwar sayar da hannayen jari ta birnin Shanghai idan aka kwatanta da hauhawarsa a bara, amma sun sake tashi na kimanin kashi bakwai cikin ɗari a ranar Litinin.

Hukumomin China suna sa ido ga kuɗaɗen da ake turawa ƙetare ko dai ta hannun bankunan zuba jari ko sayan kamfanoni ƙetare don hana bankunan shiga wata kasada musamman ta bashi. Rashin yin cinikin takardun kuɗin kasar a kasuwannin duniya shi ma yana taka rawa bisa manufar. Bugu da ƙari babban bankin China na da isassun kuɗaɗen da zai iya tallafawa bankunan ƙasar da su.