Salon rayuwaAfirka
Mata na fataucin kwayoyi a Jamhuriyar Nijar
February 27, 2024Talla
A Jamhuriyar Nijar wani abin da ke zaman kalubale ga al'ummar kasar shi ne yadda sannu a hankali mata ke mayar da hankali ga safara da fataucin kwayoyi da wasu kayan maye a 'yan shekarun baya-bayan nan, sana'ar da ke tattare da hadari wadda a can baya ke zaman abun dogaro ga mazaje.
Jami'an tsaron a jihar Tahoua sun kama wasu matan dauke da miyagun kwayoyi da ake zarfi suna safara zuwa wasu sassan kasra da ma kasashen ketere.