Matsalolin mutuwar farat-daya a Afirka
March 31, 2026
Mutuwa kwatsam ta zama babbar matsala ga lafiyar jama'a a Kamaru, wacce galibi ke da alaƙa da cututtukan zuciya da jijiyoyin jini (arrhythmias, hauhawar jini, ciwon suga, da kuma kiba. Sau da yawa, tana shafar matasa da 'yan wasa, tare da samun kamuwa da cutar da kaso 33.6 cikin mutum 100,000 ko wace shekara, galibi tana faruwa ne a gida ba tare da taimakon likita nan take ba.
Matsalar cutar
Mutuwa farat daya na kara samun gidin zaman a Afirka, Kamarun ma bata tsira ba, ciwo ne da ke kashe mutune sannu a hankali, ciwo ne da ke ci gaba da jefa likitoci cikin damuwa.
Farfesa Jerome Boomhi likitan ciwon zuciya ya ce “Za a iya bayyana mutuwa farat-daya a matsayin mutuwa da ke zuwa ba zato ba tsammani akan mutum mai nuna cewa yana cikin koshin lafiya, wannan ciwo na kara yawaita cikin al’ummarmu yana tunzura masana ilimin kimiya fannin aikin likita da bincike akan batun”
Yawancin lokuta ana dangantawa da ciwon jijiwoyin jini, mutuwa kwatsam ta kasance babbar matsala ga lafiyar jama’a a kasar Kamaru. Farfesa Felicité Kamdem mataimakiyar shugaban kungiyar likitocin zuciya ta ce babu wanda bai san hadarin da ke tattare da ciwon zuciya ba.
matsayar taron
Masana na ƙasa da na ƙasar waje sun tattauna a Douala karkashin babban taro na 15 da ƙungiyar likitocin zuciya a suka hada, don jan hankali tare da yin gargadi.
Farfesa Liliane Kuate Mfeukeu kwararriya a fannin ciwo zuciya ta ce taron zai taimaka wajen shawo kan cutar, Yayin da Kamaru ke fuskantar wannan lamari, kungiyar lokiticin zuciya na rubanya bukukuwan wayar da kan jama’a ta hanyar gwaje-gwaje a duk fadin kasar a cewar Farfesa Anastase Dzudie shugaban majalisar kungiyar likitocin ciwon zuciya a Kamaru
Amma akwai manyan kalubale a Kamaru, yan kasar na ci gaba da samun karancin damar samun kulawa daga gwamnati.