1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalolin nahiyar Afirka sun dauki hankalin jaridun Jamus

AliyuJuly 29, 2016

A wannan mako mai karewa jaridun Jamus sun duba irin matsaloli n da ke addabar kasashen Sudan ta Kudu da aiyukan yan tawaye a Somalia da Najeriya.

Hoto: picture-alliance/dpa/W. Krumm

Jaridar Neues Deutschland ta ce da alamu shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, matsalolin kasar a yankunanta dabam dabam suna nema su fi karfinsa. Kungiyoyin yan tawaye sun dukufa ga lalata bututun man fetur a kudu maso kudancin kasar da kuma hana Najeriya samun kudi daga abin da kashi 70 cikin dari na tattalin arzikinta ya dogara a kansa, wato man fetur. Idan aka kwatanta da bara, yawan man da Najeriya take hakowa ya ragu a bana da kashi 25 cikin dari, bayan ma faduwar farashinsa a kasuwannin duniya, ga kuma rikicin Boko Haram, wanda shima ba a shawo kansa gaba daya ba tukuna. A baya-bayan nan ne lokacin wani jawabi, shugaba Buhari yace burinsa shine ya tabbatar da hadin kan Najeriya, kuma zai yi iyakacin kokarinsa domin tabbatar da haka. Jaridar Neues Deutschland tace manufofin kudi da shuagaban na Najeriya ya kaddamar su ma dai da alamu ba wadanda suka dace bane. Yayin da sauran kasashe ma su arzikin man fetur suke kyale darajar kudadensu su daidaita da yadda ake samun fadi-tashi a kasuwannin man fetur, Najeriya tana ci agaba da kwatanta darajar kudinta da dollar Amirka. Kasar ta ki rage darajar Naira, ko dage takunkumin da ya hana shigar da wasu kayayyaki kasar.

Jaridun Süddeutsche Zeitung da Berliner Zeitung duka sun yi sharhi kan halin da ake ciki a Sudan ta Kudu, inda bayan fada tsakanin kungiyoyi dabam na magoya bayan shugaban kasa Salva Kiir da mataimakinsa, Rieck Machar, kasar take kan hanyar tsunduma ga yakin basasa. Jaridar ta yi tsokaci da koran mataimakin shugaban kasa Machar daga mukaminsa, inda tace: sabon mataimakin shugaban kasa da aka nada, ya kara iza wutar rikici a Sudan ta Kudu. Bayan da Rieck Machar ya tsere daga birnin Juba, shugaban kasa Salva Kiir ya nada ministan ma'adinai, Taban Deng Gai ya maye gurbinsa. Jaridar Berliner Zeitung ta kara da cewar a bayan rashin fahimtar siyasa, akwai kuma gaba mai tsanani tsakanin kabilunsu biyu. Yayin da Rieck Machar ya fito daga kabilar Nuer, Salva Kiir ya fi samun goyon bayaansa ne daga kabilarsa ta Dinka. A watan Aprilu ne Salva Kiir da Rieck Machar suka kafa gwamnatin hadin kan kasa, bayan sanya hannu kan yarjejenisyar zaman lafiya tsakaninsu a watan Agusta na bara, to sai dai wannan hadaka bata yi nisa ba. Rikici tsakanin yan siyasar biyu ya sanya kwararar duban yan gudun hijira daga kasar ta Sudan ta Kudu zuwa kasashe makwabta, musamman Yuganda.

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta yi nazari ne kan rikicin yan tawaye na kungiyar Al Shabaab da Somaliya take fama da shi. A wasu tagwayn hare-hare a farkon wannan mako a kusa da tashar jiragen saman Mogadishu, akalla mutane 13 ne suka rasa rayukansu. Jim kadan bayan wadannan hare-hare, kungiyatr ta Al Shabaab take ita take da alhakin kaisu, kuma ta yi hakan ne domin cutar da sojojin rundunar kiyaye zaman lafiya ta kasashen Afika dake Somaliya, Amisom. wadda take da hedikwatar a kusa ta tashar. Jaridar ta ce ko da shike a shekara ta 2011, bayan fada mai tsanani sojojin Amison suka kori mayakan Al Shabaab daga Mogadishu, amma kungiyar har yanzu tana mallakar yankuna masu yawa a tsakiya da kudancin Somaliya.

Shekaru 92 da haihuwa: Robert Mugabe na ZimbabweHoto: picture-alliance/dpa/A. Ufumeli

A kasar Zimbabwe, mutane suna kara janye jikinsu daga shugaban kasar, Robert Mugabe, ganin yadda take kara tsunduma cikin matsalolin tattalin arziki. Wannan dai shine sharhin jaridar Neuer Zürcher Zeitung a wannan mako. Jaridar tace bayan zanga-zanga ta tsawon makonn ta adawa da gwamnati, yanzu ma su kansu gwarzayen da suka yi yakin kwatarwa Zimbabwe yancin kanta sun fara juyawa Mugabe baya. A da can irin wadannan tsoffin mayaka ne shugaba Mugabe, dan shekaru 92 da haihuwa ya fi dogara da su domin samun goyon bayan ci gaba da mulki. Jaridar ta ce shugaban da ke mulki tsawon shekaru 36, shi yake da alhakin mummunan hali da azabar da al'ummar Zimbabwe suke sha a yanzu.