Matsalolin rashin kasafin kudi a Najeriya
May 4, 2018Duk da cewar dai an dauko alkawarin farawa tare da kaiwa ga amincewa a cikin kasafin tarrayar najeriya na shekara ta 2018 tun a watan Janairu, ana shirin share satin farko na watan Mayu a cikin jiran kasafin Najeriya na shekarar bana.
Sau dai dai har guda uku dai ana sa ran kaiwa ga amincewar kasafin sau Ukun yana zama tatsuniyar gizo gay an majalisar da daga dukkan alamu suka dau kasafin ya zuwa makami a cikin yakin dake tsakaninsu da bangaren zartarwa.
'Yan majalisar dai Allal misali sun sa kafa sun watsar da batun kasafin domin wata ziyara ta musaman ga senata Dino Melaye da ya shiga takun saka da hukumar yan sanda ta kasar.
Tun kafin nan dai dama majiyoyin fadar gwamnatin kasar na zargin kokarin neman amfani da kasafin kudin kasar a matsayin makamin neman tsayar da siyasar shari'ar shugabannin majalisar dattawan Bukola Saraki. A fadar Aliyu Sabi Abdullahi da ke zaman kakakin majalisar dattawa batun kasafin hurumi ne na wakilcin da babu gaggawa.