1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar ci rani ba kan kaida ba ga matasa

Gazali Abdou Tasawa
March 21, 2023

Makarantar horon 'yan jarida ta DW Academy ta gudanar da taron fadakarwa ga matasa a jamhuriyar Nijar hadarin tafiya ci rani ba bisa ka'ida ba zuwa kasashen Turai.

Hadarin tafiya ci rani ta barauniyar hanya
Hoto: Getty Images/C. McGrath

Makasudin taron shi ne fadakar da matasa kan illolin tafiya ci rani ba a kan ka'ida ba da kuma matakan da ya kamata matasan da ke son yin tafiyar su dauka domin kauce wa fadawa hadurra ko tarkon doka.

Daruruwan matasa ne dai maza da mata suka halarci taron gangamin wanda makarantar horar da 'yan jarida ta DW Academy ta shirya a harabar gidan radiyon Goudel wani radiyon raya karkara a birnin Yamai. A wajen taron an haska majigi na labarin wani matashi dan Ghana wanda kan hanyarsa ta zuwa ci rani a kasar Libiya ya tsinci kansa a gidan kurkuku a kasar Nijar inda ya share sama da shekara daya a bisa zargin fataucin bakin haure.

DW ta kuma yi amfani da wannan dama domin kaddamar da wani shafin yanar gizo da zai taimaka wa matasan samun cikakkun labarai kan tafiya ci rani kamar yadda Gerlind Vollmer babbar jami'ar makarantar ta DW Academy ta baiyyana.

"Ta ce shafin ya kunshi wani sashe na mahawara da ke bayani kan maudu'ai kamar rashin aiki ga matasa da damar da suke da ita ta tafiya wasu kasashe kamar na ECOWAS don neman aiki. Shafin ya kuma kunshi bayanan shaidun gani da ido na wadanda suka taba tafiya ci ranin, irin matsalolin da suka fuskanta, na bauta ko yi wa mata fyade ko tsare su a gidajen kurkuku na Libiya"  

DW Academy ta kuma sanar da shirya wata muhawara ta intanet da kuma a fa'idoji kan sanin ‘yanci da kuma hadarin da ke tattare da tafiya ci rani ba bisa ka'ida ba.